Advert
Home Sashen Hausa An bayyana kafa kotun musamman don sauraren koke-koken da suka shafi biya,...

An bayyana kafa kotun musamman don sauraren koke-koken da suka shafi biya, amsa da tara haraji a matsayin babban matakin da zai taimaka wajen habaka samun kudin shiga ga gwamnatoci.

An bayyana kafa kotun musamman don sauraren koke-koken da suka shafi biya, amsa da tara haraji a matsayin babban matakin da zai taimaka wajen habaka samun kudin shiga ga gwamnatoci.

Gwamna Aminu Bello Masari ya fadi haka yau, a yayin da ya amshi bakuncin Shugabannin wannan kotu na shiyyar Arewa maso Yamma a fadar Gwamnatin Jiha dake Gidan Janar Muhammadu Buhari a nan Katsina.

Gwamnan ya bayyana cewa rashin fahimtar da ake fuskanta tsakanin masu amsar harajin da kuma masu biyan, musamman wajen tantance yawan abinda za a biya yana zama karfen kafa wajen tara kudin harajin.

Alhaji Aminu Bello Masari ya kara da cewa dole sai al’umma ta aminta a jikinta
cewa ita ke da alhakin yanke hukunci a kan duk abinda ya shafe ta sannan za a sami ci gaban da ake bukata. Hakan kuma ba zai samu har sai tana sa hannu wajen daukar nauyin al’amurranta ta hanyar bayar da haraji a kan huldodin cinikayya da kasuwancin da take gudanarwa a yau da kullum.

Tun farko a nashi jawabin, jagoran tawagar Barista Umaru Adamu ya shaida wa Gwamna Masari cewa sun zo Katsina ne domin su gabatar da wannan muhimmiyar kotu da kuma ayyukan da take gudanarwa musamman na shiga tsakani da kuma yin sasancin domin tabbatar da cewa da mai biyan da mai amsar ba wanda ya kwaru.

Yace rashin samun koke ko daya daga jihar Katsina, walau daga masu amsa ko masu biyan harajin na cikin abubuwan da suka kara jan hankalin su wajen ganin sun kawo ziyara jihar Katsina domin tantance yadda lamarin yake gudana a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Northern Group defends suspended NPA MD, accuses Amaechi of Witch-hunt

Northern Group defends suspended NPA MD, accuses Amaechi of Witch-hunt By Saxone Akhaine, Kaduna 15 May 2021   |   4:12 am   Amaechi Arewa Youths under the umbrella of...

Mata ayi hattara: Wani mazanbaci yana amfani da social media wajen yiwa mata fyaɗe kuma ya kashesu

TURKASHI: Dubun wani matashi ta cika da ya kware wajen shigar attajirai a social media yana gayyatar yan mata wajensa da sunan zai basu...

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane Dauke Da Bundigu Da Harsashai A Jihar Zamfara

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane Dauke Da Bundigu Da Harsashai A Jihar Zamfara Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Maigirma Gwamna Matawalle ta yi nasarar...

Rikicin Isra’ila da Falasɗinawa: Su wane ne Larabawan Isra’ila?

Rikicin Isra'ila da Falasɗinawa: Su wane ne Larabawan Isra'ila? 14 Mayu 2021 Wannan makon ya kasance mai cike da rikici a yankunan Isra'ila da Falasɗin. Bayan shafe...
%d bloggers like this: