Wani bincike da aka gudanar ya bankaɗo wata badakala ta fiye da naira biliyan uku da ake zargin an yi a ma`aikatar gona ta tarayya.
Jaridar Premium Times ce ta gudanar da bincike, wadda ta gano cewa an cire kudaden ne ta hanyar saka su a asussan wasu jami`an ma`aikatar.
Jaridar ta lissafa sunayen ma`aikatan da adadin kudaden da aka saka a cikin asussan nasu, har ma da bayanin irin hidimar da aka yi ikirarin yi da kudaden