Allah Daya Gari Bamban: An Bada Sanarwar Dauke Wutar Lantarkin Kwana Daya Rak A Jamhuriyyar Nijar.

A jamhuriyyar Nijar wa su jihohi ba za su samu wutar lantarki ba a gobe Lahadi na wasu sa’o’i, amma sai da suka bayar da sanarwa a gidajen Talabijin da Rediyo har ma shafukan sada zumunta.

Ga dai abin da sanarwar ke cewa:

“A Nijar ba za a samu wutar lantarki yadda aka saba ba a gobe lahadi 07/03/21 a cikin jahar Dosso, Yamai da Tiliberi.” Inji sanarwar.

“Kanfanin Samar da wuyar lantarkin kasar NIGELEC ya ce sakamakon wasu ayukkan gyare-gyare da za su yi, wadannan jahohin za su fuskanci katsewar wuta tun daga karfe 9h na safe zuwa 19h na dare.” Sanarwar ta jaddada.

A kasarku ko ana yin haka idan ta taso, ko kuwa sai dai kawai a ce “wata miyar sai a Makwafta ne?”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here