Advert
Home Sashen Hausa An Ƙarfafi 'Yan Midiya Tare Da Gargaɗin Su Kan Saƙonnin Da Suke...

An Ƙarfafi ‘Yan Midiya Tare Da Gargaɗin Su Kan Saƙonnin Da Suke Yaɗawa A Zaurukan Sada Zumunta.

An Ƙarfafi ‘Yan Midiya Tare Da Gargaɗin Su Kan Saƙonnin Da Suke Yaɗawa A Zaurukan Sada Zumunta.

Daga Auwal Isa Musa.@katsina city news

An ƙarfafa tare da gargaɗin masu ta’ammuli da rubuce-rubuce a zaurukan sada zumunta na zamani, har ma da ‘yan jarida, dangane da rubuce-rubuce da sauran sakonnin da suke yaɗawa al’umma.

Shahararren Malamin addinin musuluncin na ɓangaren ‘yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky a Katsina, Shaikh Yakubu Yahaya ne ya yi wannan kwaɗaitarwar da kuma tsoratarwar lokaci guda, a yayin da wata tawaga ta masu ta’ammuli da zaurukan sada zumunta na zamani ( ‘yan midiya) da ‘yan jarida suka kai masa wata ziyara a ranar Lahadin nan.

Malamin ya ce; “Shi wannan ɓangare na Midiya, ɓangare ne mai matukar muhimmanci. Domin da shi ne ake juya duniya, har ma yana cikin rukunnan gwamnatocin zamani; Majalissar zartarwa, Majalissar dokoki, ɓangaren Shari’a, sai na hudunsu Midiya. Da su ake tafiyar da gwamnatocin duk duniyar nan.” In ji shi.

“Amma ku (‘yan midiya) ba ƙarya za ku yi ba; ba kuma ƙage za ku yi ba; ba kuma don ba ku son mutum za ku fadi abin da bai fada ba. Allah na cewa; “Kada ƙiyayya da mutane ta sa ku yi masu rashin adalci, ku faɗi abin da yake daidai shi ne abin da ya fi zama kusa da Taƙawa…” alamar kana jin tsoron Allah kenan. Saboda in ka faɗa; za a tambaye ka; in ma ka rubuta; za a tambaye ka!” Ya tsoratar.

Malami Yakubu Yahaya ya kuma jinjinawa ‘yan midiya musamman masu isar da saƙonnin addini a zaurukan na sada zumunta, inda ya yaba masu matuka, ya kuma ƙarfafa masu gwiwa kan haka.

“Kar ku raina abin da kuke yi, yana da muhimmanci. Allah ya san shi, kuma yana aiki da shi( wajen ɗaukaka addininsa).” Ya kwaɗaitar.

“A sa hotuna na gaskiya, maganganu na gaskiya a sa wa mutune su gani. In bidiyo ne, a sa wanda zai zama ya amfani jama’a, har su tsaya su gani.” Ya nasihantar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

TSAKANINA DA GWAMNATIN KATSINA(kashi na uku)

  Kabir sadiq (Dan Abu) A baya na tsaya inda mukayi waya da ADC kuma yaje ya gaya wa maigirma gwamna yadda abun yake, shi Bafarawa...

“My political career ends with the governorship of Rt. Hon. Aminu Bello Masari”…..Muntari Lawal

The opening caption above is his replay to us when we proposed to him to aspire for governorship race in 2019. His closing remarks...

A 39-year-old man, Ahmed Abdulmumini, has been arrested by the Katsina State Police Command for alleged cyber-stalking.

According to the police, Abdulmumini’s arrest followed a complaint by Governor Aminu Masari’s Special Adviser on Domestic Affairs, Alhaji Ibrahim Umar. Umar allegedly told the...

Tsohon Ministan Noma Abba Sayyadi Ruma ya Rasu a Birnin London

Da Dumi-Dumi: Tsohon Ministan Noma, Alhaji Abba Sayyadi Ruma Ya rasu a Birnin Landan INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN Allah yayima Alhaji Abba Sayyadi Ruma rasuwa...
%d bloggers like this: