Amurka za ta fitar da rahoton da ya shafi Yariman Saudiyya kan kisan Jamal Khashoggi-bbc

Ana sa ran gwamnatin Biden za ta fitar da wani rahoton sirri na Amurka ranar Alhamis kan ko Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman shi ya bayar da umurnin kisan ɗan jarida Jamal Khashoggi a shekarar 2018, kamar yadda wasu jami’an da suka san lamarin suka bayyana.

Fitar da rahoton ya nuna wani sabon yunƙuri na Shugaba Joe Biden na sake daidaita dangantaka da Saudiyya bayan shekaru suna ɗasawa a matsayin Amurka babbar aminiya kuma abokiyar hulɗar kasuwanci.

Biden na son sauya manufofin Amurka da dangantar tsohuwar gwamnatin Donald Trump da Yarima mai jiran gado inda yake son dawo da tsohon tsarin dangantakar ƙasashen biyu.

Mai magana da yawun Fadar White House Jen Psaki told ya shaida wa manema labarai cewa Biden zai tattauna da Sarkin Saudiyya ne kawai kuma ba da dadewa ba za a fitar da rahoto kan kisan Khashoggi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here