RANAR 17/4/1983 ALLAH (SWA) YA dauki ran Malam Aminu Kano, jagoran talakawa, jagoran NEPU a 1959 da kuma PRP a 1979. Aminu Kano, ya sadaukar da rayuwarsa wajen fafutukar neman na talaka ‘yanci da samun mafita.

Wadanda su ka zo su ka yi wayau a zamanin sa sun san ko wanene shi, sun san nauyin sa. Mu da mu ke kanana a lokacin ba mu san shi, da irin nauyin sa ko zafin hannun sa ba.
Lokacin da na tafi wajen Alhaji Rabe GNPP Funtuwa domin yin hira da shi akan zancen siyasar Shata a Funtuwa cikin 2010, sannan na ida sanin hakikanin wanene Malam Aminu Kano. Sa’adda na kammala hira da shi akan alakarsa da Shata sai na ajiye takarda da biro. Na ce ma sa, ‘to yanzu an gama zancen Shata, ina so in yi ma ka tambaya akan siyasa, na zaben da ya gabata’
Na ce ma sa ya aminta da zaben da aka yi na 2007 koko bai aminta ba? Domin, ni, abin na ci-ma ni tuwo a kwarya. Sai ya yi shiru. Na sake nanata magana, ya yi shiru. Sai mutanen da suka taru don jin labarin Shata su ka ce ma sa: ‘Ka na fa ji, ka amsa masa tambayarsa’
Sai ya ce ma ni: ‘To ka fada ma ni, tun daga zamanin NEPU da NPC ya zuwa yau din nan, wa ka ga ya ci zabe ba tare da magudi ba? Sai na ce masa ‘kamar yaya, ni dai ban zo ba lokacin zaben NEPU, amma har shi ma magudi aka yi? Ya nuna ma ni tabbas, a zabe na biyu na 1964 an shirya ma NEPU magudi, wanda ya ja Aminu Kano bai samu kujerar shugaban Kasa ba. Ya ce ma ni a lokacin, an yi amfani da eja wajen kai Aminu Kano kasa. Ya ce, idan aka kada kuri’a sai kowa ya tafi. Amma, a fadin Arewa kaf, NEPU ta samu rinjaye na ban mamaki. Saidai kashhhh!!. Eja, su suka canza takardar fosta ta ‘yan takara ta hanyar canza ko musanya fostar su a kan akwatuna. Wato, kafin kidaya, sai aka dauki fostar NEPU aka dora ma jam’iyyar adawa da ke da manya a Arewa. Ita kuma fostar ta , watau ta masu takarar ta, aka sanya ma akwatuna na NEPU. Da aka zo kidaya, sai ga kuri’ar NEPU ta koma hannun jam’iyyar adawa. To, da aka fitar da sakamako sai talakawan Arewa su ka bukaci Aminu Kano ya kai kara kotu. Kuma, idan aka kai kara kotu, to amshe nasarar za’a yi a ba su. Sai ya ce : ‘a’a, shi da shugaban jam’iyyar adawa irin manufofinsu daya ne, watau manufar ciyar da Kasa gaba, tare da kawo muhimman abubuwan da za su kawo ma talaka mafita.
Aka yi, aka yi da shi amma atafau, MALAM Aminu Kano ya ce ba za ya je kotu ba, ya bar ma Allah. Ya ce, shi da Sardauna, manufar su duk guda ce.
Wannan shine jawabin Rabe GNPP. A rannan na ida gane wanene Aminu Kano.
Toh, a yau, kwamacala ta yi yawa. Kwadayin mulki mulki ya hana ‘yan jam’iyyar adawa su bari wadda ta samu nadara ta kai talaka inda ya kamata ta kai shi.
A yau, an wayi gari masu adawa sun kunno kai sun shigo da fitintinu da masifu sun cusa sin hana kasa ta zauna lafiya. A waccan siyasa a kunno da Boko Haram. A wannan siyasar an kunno da kidnapping, watau satar mutane domin amsar kudin fansa. Wannan duk adawa ce ta kawo haka. Sun kasa hakuri, su rufa ma jam’iyya mai CI ta kai ga nasarorinta. Jihohin arewa-maso-yamma na cikin tashin hankali na rashin tsaro. An ce manyan mu na a bayan wannan fitina, amma an ki bayyana su.
A iya nazari, sauran Kasashen AFIRKA, wasu daga cikinsu na fama da irin wannan matsala. To shin wai, mi ya bambanta Aminu Kano da ‘yan siyasar mu na Afirka na yau? Su, ba su da yafiya ne? Ba su iya daukar kaddara da dangana kamar wanda Allah Ya ba Aminu Kano?
Allah Ka jikan wannan bawa na Ka, Ka gafarta masa. Allak Ka kyautata makwancinsa. Allah Ka sanya a samu jajirtattaun ‘yan siyasa ma su kauna da kishin Kasa a zucci.

Dokta Aliyu K. IBRAHIM ya rubuto daga Katsina.
Lahadi, 17/4/2022

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here