Amaechi ya ayyana aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa

Amaechi

Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya sanar da aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Amaechi ya ayyana takararsa ne a wani taron siyasa a Fatakwal a ranar Asabar.

“Na tsaya a gabanku yau don bayyana aniyata tare da gabatar da bukatar zama shugabanku na gaba,” in ji shi.

Yanzu Amaechi da tsohon gwamnan Legas Bola Tinubu da gwamnan Kogi Yahaya Bello ne suka fito suka ayyana takararsu ta shugaban ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here