Al’ummar Jihar Katsina Suka Nemi A Dawo Da Haraji Da Jangali Ba Buƙatar Gwamna Masari Ba Ce, Cewar Kwamishinan Kasafin Kuɗi, Alhaji Lawal Jobe

Kwamishinan Kasafin Kuɗi Da Tsare-tsaren Tattalin Arziki Na Jihar Katsina, Alhaji Faruq Lawal Jobe ya bayyana cewa maganar haraji da Majalisar Zartaswa ta jihar Katsina ta amince da shi ba fa ra’ayi ko bukatar Gwamnan Jihar Katsina ba ce, al’umma jihar Katsina ne da kansu suka baiwa gwamnatin jihar Katsina shawara domin magance matsalar tattalin arziki da jihar Katsina ke fuskanta.

Faruq Lawal Jobe ya bayyana haka ne lokacin da ya yi wata hira ta musamman da Jaridar Blueink News Hausa a ofishinsa da ke tsohan gidan gwamnatin jihar Katsina, a yau Litinin domin yin karin haske game da harajin dubu biyu-biyu ga kowane mazaunin jihar Katsina da ya kai shekara goma sha takwas da kuma jangalin dari biyar ga sa ko saniya da majalisar Zartaswa ta amince a biya a kowacce shekara.

Kwamishinan Kasafin Kuɗi Da Tsare-tsaren Tattalin Arziki Na Jihar Katsina, ya ci gaba da cewa a lokacin da mu ka zo karo na biyu tattalin arziki ya fara taɓarɓarewar, kuɗin shigar da muke samu ya yi karanci, saboda cutar nan ta mashako, mun zagaya kowacce karamar hukuma talatin da hudu da muke da su domin mun ga Cewar kasar nan za ta shiga wani yanayi na rashin kudi. A cikin wannan gabar ne muka zagaya kowacce karamar hukuma domin tattara shawarwarin neman hanyar kudaden shiga, da za’a yi wa al’umma Aiki, sai jamaa suka ba da shawarar a bullo da haraji da jangali kamar yadda ake yi a da. A cikin rahotan da muka gabatar ga gwamnati, bayan zagayen da muka yi ga bukatar da al’ummar jihar Katsina gabatar su ka zo da su da kuma alfanun da za’a iya samu a wannan bangare, anan ne Maigirma Gwamna ya kai shi gaban majalisar Zartaswa ta jiha da yake shugabanta, inda majalisar ta aminta a sake kafa wani kwamiti da zai kara zagaya wa a kowacce karamar hukuma talatin da hudu a tara masu ruwa da tsaki ayi masu bayani filla-filla dangane da wannan bukatar na dawo da haraji da jangali kuma wace shawara za su bayar wajen ganin an aiwatar da shi, masu ruwa da tsaki da muka tattara suka aminta. Ina son al’umma su sani dawo da haraji da jangali ba tunani ba ne na gwamna Masari, al’umma suka bukaci haka. A cikin kananan hukumomin talatin da hudu, ashirin da takwas duk wanda ya tashi ya yi jawabi ya goyi bayan a maido da haraji da jangali, sun kuma ba da shawarwarin yadda za’a tafiyar da su, kananan hukumomin shidda ne kacal muka samu banbanta ra’ayi. A takaice dai wannan rahoto muka tattara, muka sake gabatar da shi gaban majalisar Zartaswa Jihar Katsina, a zaman da aka yi satin da ya gabata aka ce gwamnati ta aminta duk wani wanda ke zaune a jIhar Katsina, da ya kai shekara goma sha takwas to zai biya harajin dubu biyu a karshen kowacce shekara, mata kuma sai wadda ke aikin albashi kadai za ta biya, sa ko saniya kuma dari biyar.

Daga karshe, kwamishinan ya bayyana cewa wannan haraji da jangali, haraji ne na raya kasa kuma an bullo da tsare-tsare masu kyau don ganin an gudanar da muhimman ayyukan raya kasar kuma aka tura wannan bukatar gaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, domin ganin ya zama doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here