Advert
Home Sashen Hausa Al'umar Katsina sun koka game da ƙarancin Ruwan sha...

Al’umar Katsina sun koka game da ƙarancin Ruwan sha…

Al’umar Katsina sun koka game da ƙarancin Ruwan sha…

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Wani layin masu ibar ruwa

Karamar hukumar Katsina Itace karamar hukuma mafi girma a cikin Ƙananan hukumomi 34 na jihar ta Katsina. Kuma nan ne Babban Birnin Jihar katsina inda Gwamna da duk wani mai ruwa da tsaki a Gwamnatin jiha suke zaune, da iyalan su.

Amma al’ummar yankin suna fama da matsanancin rashin ruwan sha duk da irin ƙoƙarin da Gwamnati take cewa tana yi wajen samar da ruwan, ta hanyar yashe Dama-damai, da samar da Injinan tace ruwa na zamani.

Ko a watanni da suka gabata Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci garin Dutsin-ma inda ya buɗe wani katafaren Dam, wanda yana ɗaya daga cikin muhimmai da ke bawa Katsina Ruwa.

A ina matsalar take…?

Mun tattauna da wasu Al’umma na Unguwannin cikin Birnin Katsina, irin su Unguwar Unwala. Gwabron gida kofar Soro Saulawa, Marnar kadaɓo, kofar Guga, zuwa kofar ‘yan Ɗaka, duka Zancen guda ɗaya ne. “Bamu da ruwa, rabon da muga ruwan Famfo har mun manta”

Da wakilin Katsina City News yake zantawa da wani Dattijo Mazaunin Unguwar Unwala ya sheda mana cewa, su indai batun Ruwan famfo ne, sun yanke ƙauna, saboda sunyi kwamiti sunje ma’aikatar Ruwa, yafi a ƙirga amma ba’azo aka duba matsalar ba ballantana a saran magance masu ita, “yace yanzu duk girman Unguwar nan Famfon Buga ƙato guda biyu ne muke amfani dashi, shima guda yana yawan lalacewa, ga kayansa da tsada amma babu mai taimaka mana a gyara, sai wani makwafcin mu mai wancen gidan” (ya nuna wani gida dake kusa da inda muke tattaunawa dashi) In kanada Kuɗi ka siya, in baka da kuɗi kayo sakko kabi layi a buga kato, ka samu na Al’wala, Injishi.

Haka abin yake a Unguwar Gambarawa duk acikin Birnin Katsina, inda aka sheda mana, rabon da wani abu wai shi ruwan Famfo yazo tun a zamanin Gwamnatocin baya, “Harkwamiti munyi munje munkai ƙorafi, koda yake anzo Unguwar an duba, amma ba’a iya gyara matsalar ba” inji wani daga cikin manyan Unguwar.

Inda matasan da muka tattauna da su, suka ce….”Ita dama wannan Gwamnatin fadi take amma ba aiki, idan da abinda suke fadi a baki suna aikatawa da garinmu ya zama birnin London.

Gwamnatin Katsina a karkashin jagorancin Aminu Bello Masari a kwanakin baya ta samar da Injina na miliyoyin Nairori, gami da gyara ma’aikatun na ruwa da yima tsofin injina garambawul, amma bisa dukkan alamu kwalliya bata biya kudin sabulu ba

 

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WATA SABUWA: Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki auren budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi...

Rundunar Yansanda Ta Jihar Katsina Ta Chafke Daya Daga Cikin Yan Bindiga Da Suka Hallaka Hakimin Yantumaki.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai...

THE DUALIZATION OF THE IBADAN – ILORIN EXPRESSWAY AND SECTION II OF THE OYO – OGBOMOSO ROAD BY THE BUHARI ADMINISTRATION IS ALMOST DONE!

#PositiveFactsNG In staying true to its passionate commitment to developing Nigeria's infrastructure, do you know that the dualization of the Ibadan - Ilorin Expressway as...

THE APAPA – OSHODI – OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING!

https://www.facebook.com/Do-You-Know-NG-101788642037662/ THE APAPA - OSHODI - OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING! #PositiveFactsNG Do you know that the reconstruction project of the Apapa - Oshodi...

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News 6/12/2021 Kungiyar Mafarauta ta Najeriya, wato Hunters Council of...