Advert
Home Sashen Hausa ALMAJIRAN EL-ZAKZAKY SUN TUNA DA RANAR 12 GA WATAN 12 A KATSINA.

ALMAJIRAN EL-ZAKZAKY SUN TUNA DA RANAR 12 GA WATAN 12 A KATSINA.

ALMAJIRAN EL-ZAKZAKY SUN TUNA DA RANAR 12 GA WATAN 12 A KATSINA.

Ibarahim Yaqub @Katsina City News

Da safiyar Ranar Asabar 12/12/2020 ne ‘yan’uwa Musulmi almajiran Malam Ibrahim El-Zakzaky, suka fito domin tunawa da kisan da sojojin Najeriya suka yi wa danginsu a shekara ta 2015.

Ɗaruruwan mabiyan El-Zakzaky ne na katsina suka fito maza da mata ɗauke da hotuna na jagoran nasu tare da wasu hotunan da ke ɗauke da abinda ya faru a irin wannan rana. Haka kuma suna tafe suna rera take kala-kala na nuna alhini da takaicin abinda aka yi masu.

Masu Jerin gwanon dai sun taso ne daga unguwar madawaki, sannan suka bi ta sabon titin darma har zuwa titin rafin dadi. Daga nan suka ɓilla ta sabon layi zuwa gwangwan. An ƙarƙare wannan jerin gwano a bakin library kusa da babban Masallacin Juma’a na Katsina.

Da yake jawabin kammalawa Malam Yakubu Yahaya Katsina ya faɗi maƙasudin fitowwarsu, inda ya ce; sun fito ne domin bayyan irin zalincin da aka yi masu da kuma kira ga gwamnatin Najeriya ta sako Malaminsu da ake tsare dashi tsawon shekaru biyar ba tare da wani kwakkwaran dalili ko laifi ba. Haka kuma Malamin ya bayyana irin abinda ya faru a irin wannan rana inda ya kada baki ya ce “an kashe mana aƙalla mutane sama da 1000, sannan aka ƙona wasu da rai, sannan gwamnatin kaduna ta bizne wasu 347 a ramin bai ɗaya, akwai ma, yayar Malam El-Zakzaky da aka ƙona da ranta tare da wasu matan” inji shi.

An kammala wannan jerin gwano lafiya an tashi lafiya.

– In dai ba a manta ba a shekarar 2015 ne aka tashi da wani tashin hankali wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka da dama na almajiran El-Zakzaky tare da rusa Muhallan taruka da makaranta gami da gidan Malamin bayan an harbeshi, shi da mai dakinsa Malama Zinatu. Har wa yau Malamin na a tsare a hannun jami’an tsaro duk da halin rashin lafiya da harsasai da ke jikinsu. Sannan gwamnati ta ki basu damar neman magani duk da tuni wata kotu ta ce a sake su basu da laifi kuma a biyasu diyya kuma a gida masu gida inda suke so. Amma dai gwamnati tayi fatali da dokar kotun.

Shin ko yaushe za a saki wannan Malami na addini da ake tsare dashi ko don ƙara samun zaman lafiya duba da yadda ƙasar ke ta, faɗawa halin rashin tsaro?.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

GWAMNATIN BUHARI TA KADDAMAR DA SABON TSARIN AIKEWA DA SAKO NA ZAMANI #GaskiyarLamarinNijeriya

KokunsanKo kun san cewa, a kokarin Gwamnatin Shugaba Buhari na ingantawa da zamanantar da tsarin aikewa da wasiku da sakonni, Hukumar Aika Sakonni ta...

Community leaders seek rehabilitation of dilapidated schools in Katsina

Some community leaders in Sake Gari and Ganuwa villages, Charanchi Local Government Area, Katsina State, have called for the rehabilitation of dilapidated public primary...

Masari’s Silence, Governorship Primary, Put APC on Edge in Katsina

Masari’s Silence, Governorship Primary, Put APC on Edge in Katsina With heightened insecurity, worsening economic challenges, poverty and lack of administrative direction and developmental projects,...

FG in collaboration with Kano State Government has flagged off the National Livestock Breed Improvement programme #PositivefactsNG

DoyouKnwoNGAccording to Boss Mustapha secretary to the federation who posted in his tweeter account, The Federal Government of Nigeria through Federal Ministry of Agriculture...

Buhari’s Seven Years of Delivering Affordable Housing to Nigerians through FMBN #PositivefactsNG

DoyouKnwoNGThe Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) has delivered record-breaking achievements in the seven years of the Buhari administration. Across all corporate indicators the...
%d bloggers like this: