Ali Ƙwara Azare ‘mai kama ɓarayi’ ya rasuhttps://www.katsinacitynews.com

Allah Ya yi wa fitaccen mutumin nan mai kama ɓarayi a Najeriya Ali Ƙwara Azare rasuwa a yau Juma’a.
Ali Ƙwara ya rasu ne a Abuja bayan ya sha fama da jinya.
Ya rasu ya bar mace daya da ƴaƴa huɗu sai kuma ƴan uwa masu ɗan dama.
Marigayin haifaffen Azare ne da ke ƙaramar hukumar Katagum a jihar Bauchi.
Ya yi fice sosai wajen kama ɓarayi a dazuzzukan, sannan daga bisani ya ladabtar da su da kuma koya musu sana’o’i.
Ƴan uwansa sun sanar da cewa za a yi jana’izarsa a garin Azare.