Danjuma katsina  @Katsina City News

A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala.

Bayan na dawo na tsara wa kaina fara harkokin sana’o’i da za su kawo mani kudin shiga. Na bude shagon K. BUSINESS PLAZA a ginin Mai Kudi Abdullahi da ke Kofar Kaura. Ni ne mutum na biyu da na fara kama haya a ginin. Lokacin wajen gefe daya duk daji ne.

K. BUSINESS PLAZA, muna ayyukan dab’i da fotokwafi da sauransu.

Wajen shi ne Business Centre na zamani da aka fara budewa a cikin Katsina.

Kwamfuta shida na sa da sauran kayan Business Centre. Ga katon janareto.

A lokacin muna iya kai karfe 1:00 na dare muna aiki. Daga baya muka fara ayyukan daba’i (printing). Ni na fara plastic ID card a katsina
Mutum na farko da ya fara bani aikin buga almanac shine injiniya muttaqa Rabe Darma. Wanda ya fara bani buga littafi shine salisu majigiri na tarihin garin mashi.wanda ya fara bani kalanda shine Dahiru bara u mangal,ta kamfanin Afdin.
An bude wajen a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2001. Na ci gaba da TAFIYE-TAFIYE na wasu ayyukan da Marigayi Alhaji MD Yusufu kan sa ni,cikin kasa da waje. amma nan ne ofis dina na Katsina.

A shekarar 2007 na canza sunan wajen daga K. Plaza zuwa Matasa Media Links, kuma a shekarar muka fara buga Mujallun Matasa.
Domin zaburar da matasa sun San ciwon kansu.

Yau aikin gadar kasa da gwamnatin Jihar Katsina za ta yi, ya jawo an kulle duk hanyoyin zuwa ofis dina da na shekara ashirin da watanni.

Kuskuren farko da na yi, a shekarar 2003 Gwamnan lokacin Marigayi Umaru Musa Yar’adua muka hadu a wani gida a Abuja. Ya ce in rubuto a ba ni fili in gina ginin dindindin. Ban yi ba.
Lokacin ya bani wani aikin fassara dokokin musulunci da jahar ta kaddamar da kuma buga su a jaridar Al mizan.na amshi aikin amma ban Nemi filin ba.

Haka nan a shekarar 2011, mun hadu da Gwamnan Katsina na lokacin, Ibrahim Shema a ofis din wani babban mutum a Abuja, shi ma ya ce in rubuto bukatar fili zai ba ni in gina ofis din kamfanina. Ban yi ba.
Shima a lokacin ya bani wani aiki na buga wani littafin aikin hajji da Ummara. Nayi aikin amma ban Nemi filin ba.

A shekarar 2012, MD Yusufu ya ce min ka tashi daga wannan shagon ka nemi ofis. Na ce to Yallabai. Amma ban yi ba.
Har yana cewa wannan ka bar ma yara su fara wata sana a.a lokacin har ya kawo kudi masu yawa ya bani.amma ban bi shawarar sa ba.

Yau da na ga yadda ofis din nawa ya koma ba ta inda za ka isa da mota, sai na sake tuno abin da ya faru a baya. Sai kwalla ta cika min idanu. Na ce Allah ka raba mu da ranar nadama.

A rayuwa mutum kan yi wani kuskuren da in ya farga sai ya yi kwalla. Yau na yi wannan kwallar.

Daga ofis din nan an yi abubuwa da yawa ga Kasa da Jiha.

Ya taba zama kamar ofishin wucin-gadi na kungiyar ‘yan jarida (NUJ) ta Jihar Katsina.

Duk wanda ya zo garin, nan wurin zai yi wa tsinke.

Ya taba zama wurin haduwar ‘yan gwagwarmaya daban-daban na na kasa in sun zo Katsina. Ya taba zama, ya taba zama…ya taba zama …..

Yanzu farko za mu zama ba sukuni har a gama aikin. In an gama aikin, ko wurin zai yi dadin zama a matsayin ofis?

Kafin nan, insha Allahu mun mika al’amarinmu ga Allah. …..
Muna neman ya bamu mafita..
Jaridun mu da mujallun mu suna ta bunkasa zamu shiga sabon shafi …

Danjuma katsina shi ne mawallafin jaridun Katsina City News, Jaridar Taskar Labarai da The Links News.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here