Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa Shugaban Kamfanin Zirga-zirgar Jiragen Sama Na Max Air, Alhaji Ɗahiru Barau Mangal shi ne kashin bayan jam’iyyar APC a Jihar Katsina.

Gwamna Masari ya bayyana haka ne a wata Liyafar cin abincin dare na Kungiyar Shugabannin Majalisar Dokokin Jihohin Najeriya ta shirya a gidan gwamnatin Jihar Katsina a taron su da suka saba yi duk shekara, wanda a wannan karon suka shirya taron a Katsina, wanda ya samu halartar kafatanin Shugabannin Majalisar Dokokin Jihohin Najeriya da aka kammala a jiya Asabar.

Masari ya ci gaba da cewa “ga wadanda wannan shi ne karon farko da suka ziyarci jihar Katsina, mu anan jihar Katsina da muke jam’iyyar APC, shine kashin bayan mu kuma jagora na daya a jihar Katsina kuma ana kiransa Janar Ofisa Kwamanda, bayan kammala zaɓen 2015 lokacin da shugaban kasa Buhari ya zo ya ce an masa karin girma zuwa Fild Mashal, har ila yau, shi ne mamallakin kamfanin Zirga-zirga Jiragen Sama na Max Air” cewar Masari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here