Tsofaffin Ma’aikatan Gwamnati za su yi murmushi, za a biya su kudinsu – inji PenCom

Hukumar fansho ta ce har magada za su karbi kudin da iyayensu ke bin gwamnati

Gwamnatin Buhari ta yarda a biya Ma’aikatan da su ka yi ritaya hakkokin kudinsu

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da bukatar da PenCom ta kawo masa

Za a biya tsofaffin ma’aikatan gwamnatin tarayya hakkokin kudin da su ke bi

Hukumar PenCom ta ce karin albashi da aka yi zai yi tasiri a kudin da za a biya

Jaridar This Day ta kawo labari cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da rokon da hukuar fansho ta kasa watau PenCom ta gabatar a gabansa.

Hukumar PenCom ta bukaci a ba ta dama ta biya bashin kudin da tsofaffin ma’aikatan gwamnatin tarayya su ke bi bashi a karkashin tsarin fanshon CPS na kasa.

A wani jawabi da PenCom ta fitar a ranar Laraba, ta ce an ware kudin da za a biya mutane hakkinsu.

Hukumar ta ke cewa za ta biya wadanda su ka yi ritaya daga gwamnatin tarayya ba tare da sun karbi fansho da kudin sallama ba, da kudin wadanda su ka rasu.

Sabon tsarin mafi karanci albashi zai shafi fansho

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma amince da biyan karin kudin da aka yi a kan tsarin mafi karancin albashi, wanda wannan canji ya sa fanshonsu ya karu.

A shekarar da ta wuce ne gwamnatin tarayya ta kawo sabon tsarin albashi inda kowane ma’aikaci ya koma tashi da akalla N30, 000, a maimakon N18, 000.

Kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto, za a fara biyan wadanda su ka yi ritaya daga aiki daga Yulin 2014 da 10% na abin da suka tara a asusun fanshonsu.

Jaridar ta ce hakan na zuwa ne bayan hukumar fanshon PTAD ta karbo fam Euro miliyan £26.5 daga Birtaniya, Wannan kudi sun kai Naira biliyan 13 a kudin gida.

Rahotan Matattarai Labarai ..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here