Home Sashen Hausa ALBASHIN SANATA MILIYAN GOMA .? Daga Umar tata

ALBASHIN SANATA MILIYAN GOMA .? Daga Umar tata

Abdullahi Umar Tsauri TATA

ALBASHIN SANATA MILIYAN GOMA .?
Daga Umar tata

 

A jiya muna hira da wani legislative Aide na wani Sanata na jihar Katsina, shine yake gaya mani cewa albashin Sanata a duk wata Naira miliyan goma sha ukku ne da wasu daruruwa a sama. Na rike baki da jin haka kuma na ciji dan yatsa na. Haka nan nayi ta wahalar neman kujerar Gwamna don ina gani cewa kujerar Sanata bata iya rika mani ayyuka na da nike yi kuma nike da kudurin ci gaba da yi a cikin jihar Katsina. Ashe kujerar babba ce!

Na tabbata da wannan albashin, duk watan duniya sai nayi masallaci, ko islamiyya ko in gina primary mai aji guda biyu. Na tabbata da wannan albashin kadai Makarantun primary na constituency dina sun gama karewa ace sai mun jira gwamnati ta rufe su. Na tabbata da wannan albashin yaran primary na constituency dina sun gama zama kasa a cikin aji. Na tabbata da wannan albashin zan rage matsalar aure a cikin jiha ta ga maras sa karfi. Na tabbata da wannan albashin zan iya aje Naira miliyan biyu duk wata domin taimaka ma matasa masu son sana’a da karatu a cikin gunduma ta.

Tabbas miliyan daya zata iya ciyar dani da iyali na duk wata sauran kuma mu baiwa Allah da bayin shi. Shiyasa mace mai son duniya bata iya aure na kuma ko ta aure ni sai ta fita!

Sauran kuce kujerar Sanata nike nema! Ni Gwamna nike so!
Tata tsohon Dan takarar gwamna ne a jamiyyar PDP mun dauko rubutun daga shafin sa na Facebook

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

YANDA ZAMAN KOTUN MAHADI SHEHU DA MUSTAFA INUWA YA GUDANA A BABBAR KOTUN DUTSIN-MA

YANDA ZAMAN KOTUN MAHADI SHEHU DA MUSTAFA INUWA YA GUDANA A BABBAR KOTUN DUTSIN-MA Da misalin karfe 10:20 na safiyar yau Litinin, Alkalai uku sun...

PRESIDENT BUHARI RECEIVES FMR VP ARCH NAMADI SAMBO ON NIGER ELECTION.

PRESIDENT BUHARI RECEIVES FMR VP ARCH NAMADI SAMBO ON NIGER ELECTION. President Muhammadu Buhari receives the Former Vice President Arch Namadi Sambo on the Republic...

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE?

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE? muazu hassan @ jaridar taskar labarai Gobe za a kai mahadi shehu Wanda yan sanda suka kawo daga Abuja...

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity By Bello Hamza, Abuja The group under the aegis of initiative for coalition and rights protection a not...
%d bloggers like this: