AL’AJABI: Wata Kurma Ta Musulunta A Hannun Sheik Dahiru Bauchi

Wata Baiwar Allah Kurma ta karbi addinin Musulunta A Hannun Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA a jihar Kaduna inda yake gabatar da karatun tafsiri duk shekara. Shehin Malamin ya yi mata bayanin yadda addinin musulunci yake ta bakin mai maganar kurame.

Bayan ta musulunta ta canza sunan ta zuwa Nana Khadijah.

Allah Ya karfafi duga-duganta akan wannan tafarkin na musulunci, ya karawa Shehu lafiya da nisan kwana. Amin.

Daga Othman Muhammad
Fityanu Media

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here