MATAN MARIGAYI ALAFIN NA OYO SUN ZAMA HAJA A KASUWA….

DAGA Shafin Arewa Media

Jaridar Vanguard ta ruwaito kwana uku da rasuwar Babban basaraken yarbawa, Alafin Na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi,majalisar Sarakunan Jihar Oyo ta sanar da cewa Matan marigayin su goma sha takwas 18 yanzu Suna kasuwa ga mai bukatar Aurensu ba tare da an yi musu tsarkakewar Al’ada ba.

Sai dai wannan garabasar ta haramta ga Mazaunin jihar ta Oyo da wanda aka haifa a Jihar,inda matan na marigayi Alaafin za su kwashe dukiyoyin da suka mallaka tare da shi zuwa wani bigire dake wajen jihar inda za su sake sabuwar Rayuwa.

– Saifullahi Lawal Imam

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here