Alaƙata da Dakta Mamman Shata Katsina… Alhaji Abashe, Mutumin da ya fara yin sana’ar Hoto a Katsina.

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

“Na fara zuwa Makka a shekara ta 1970 tun ana biyan Fam 112 da Sule 12 nake zuwa Makka kuma du a dalilin Sana’ar daukar Hoto ne, Ina godiya ga Allah da yayi mani wannan Baiwar Alhamdulillah!  Shekaru hamsin ina sana’ar Hoto ban taba samun ci baya ba.

Batun kalu bale, na rayuwa dama ita rayuwa ba’a rabata da shi, sai dai ni gare ni kalu bale ne ga matasa da yanayi zamani, ko ince masu duk wata sana’a da ka iya koya, don al’uma. A zamanin da, lokacin idan za’a kawo maka yaro ya koyi sana’a biyan kuɗi ake ka kowaya yaro, amma yanzu, kai zaka koyama yaro, kuma kai zaka biyashi…

To amma Alhamdulillahi, sauyin zamani ne, wannan kuma kai da zaka koyawa yaro ka ƙaru kuma ƙasa ta ƙaru ka taimake shi ka rabashi da Zaman banza”.

HAƊUWA DA SHATA: “Shata yayi mun waƙa a Shekarar 1973 lokacin yaƙin Biyafara, asalin haɗuwata da shi, watarana wani Soja yazo dashi a Kantina, zanmashi (Sojan) Hoto, alokacin idan mukayi hoto sai bayan kwana daya muke wankewa, sai Sojan yace don Allah yanaso in masa yau inbashi zai tafi dashi Lagas yakai a ma’aikatar su. Sai nayi masa ba’afi Mintina 15 ba na wanke hoton na bashi, sai shata yake tambayata ni Bahaushe ne…? nace masa Eh, ni haifaffen Kofar Guga ne, cikin garin Katsina. Anan dai yayi ta mini tambayoyin ina bashi amsa bayan yagama tambayoyin shi sai nace mashi,

“Ba mu kananan ‘yan kasuwa ba, manyan Kamfanoni da manyan mutane suna so suyi sabo dakai.  Sai Dakta Mamman Shata yace to ni ba kudinka nake so ba, akwai kayan da nakeso kayimani Hoto dasu, na Jami’ar Amadu Bello data karramani, idan na koma zan dauko su kayimun hoto dasu” nace nayi al’kawarin yin wannan Hoto.

Haka da yin wannan Maganar ankai shekara biyu, ba’a samu anyi wannan Hoto ba.

Kuma duk inda muka hadu da Shata sai ince mashi, kana bina bashi, har yanzu ban biya ba.

Watarana alokacin Jihar Kaduna, yankin Kaduna nada karamar hukuma bakwai yankin Katsina nada Karamar Hukuma bakwai, ana shirya wasan gargajiya na duk shekara, sai bana Allah yasa a Katsina za’ayishi, aka hadu a Filin Kwallo (Stadium) alokacin Matawalle Musa, Uban Ummaru musa Shine Ciyaman na Katsina, sai Sarkin Musawa Liman yayan Usman na goggo shine  Ciyaman na Dutsinma, duka sun zo wajen taro Sarkin Katsina yazo sarkin Daura yazo, Shata ma yazo, duk da shata baya cikin Program din amma saboda Kwarjininsa sai aka sanya shi, karshe, saboda ko wane irin taro ake indai shata ya kasance a farko to da yagama wakarshi taro ya tashi, shiyasa ba sanya shi farko.

Anan ne naje da Kyamara mai dauka sha biyu nayima shata hoto, kafin yagama ya dawo masaukinshi har na wanke hotuna na shiryasu nayi masu Frame, na kai masa a masaukinshi na busa gado na ajemashi…….”

Katsina City News ce ta ta Tattauna da Alhaji abashe mai Hoto ‘yar’adua Katsina. Mutum na farko da ya fara sana’ar daukar hoto a garin Katsina… Domin ji da ganin ƙasashen firar daga bakinsa, sai ku garzaya a YOUTUBE din mu Mai suna KATSINA CITY NEWS TV.

Jaridun Katsina City News, The Links News, Jaridar Taskar Labarai, na Busa yanar gizo a www.katsinacitynews.com da www.thelinksnews.com sai www.jaridartaskarlabarai.com muna buga Mujalla (Magazine) duk karshen wata wadda take fitowa da abubuwan ban al’ajabi da ban mamaki, tarihi, tattaunawa da shuwagabannin jami’o.i na Jihar Katsina, da kuma Tarihi.

Zaku iya sauke Application din mu na Android ta Playstor a wayoyin ku…kawai ku shiga Store din ku kuyi searching na KATSINA CITY NEWS, zai bayyana sai ku sauke muna da tsare-tsare daidai da zamani, aciki zakuga Sashen shirye-shiryen mu na RADIO, Podcast, TV, PAGE, Instagram, da Twitter.

Don karin bayani ☎️07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here