Barayin Daji na cigaba da kai harin sari ka noke a ƙananan Hukumomin Danmusa da Safana, Inda ko a daren Jiya Barayin sun kai hari a ƙaramar hukumar Danmusa suka kashe kimanin Mutane Biyu basu ji basu gani ba a kan hanya tsakanin yantumaki zuwa tashar mai Alewa duk a cikin ƙaramar Hukumar ta Danmusa.

Kazalika sun shiga har cikin gari a wata Unguwa mai suna kukoki nan ma suka kashe Mutum guda sukayi awan gaba ba tareda samun tirjiya ba.

Su dai Mutanen da aka kashe sun taso ne daga yantumaki zasu koma cikin Garin Danmusa inda aka bude masu wuta aka kashe su har lahira.

Dama dai ko kafin sallah da ta gabata sunje gidan wani Bawan Allah mai suna Alhaji Lawal yaro suka kashe shi har lahira.

Haka Lamarin yake a ƙaramar hukumar Safana Inda suka sace wani Manomi da Ɗan shi suka buƙaci da abasu kuɗin Fansa, bayan nan kuma suka yi masu kisan Gillah.

Ko dai abaya bayan nan Gwamnan Jihar Katsina ya Umarci Al’ummomin da suke zaune a yankunan da rashin tsaro yake addaba dasu tashi su kare kawunan su kada su zauna a riƙa kashe su kamar Ƴan Adam ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here