Akwai yiyuwar ba za’a biya Albashin Ma’aikata ba a watan Mayu…

Akwai yiyuwar ba za’a biya Albashin Ma’aikata ba a watan Mayu…

Kampanin Mai na NNPC ya aikewa da Babban Akawun ƙasar nan Takardar cewa kwabo bazasu bada ba a Matsayin haraji a wannan watan ba, abunda ke nuna cewa harajin da aka saba badawa ayi Kasafin Kudin wata wata a rabama Tarayya, Jahohi da ƙananan Hukumomin ƙasar nan ya samu tasgaro.

A takardar da Shugaban Kampanin na NNPC Mele Kyari ya aikewa babban akawun yayi bayanin cewa harkar biyan tallafin kudin Man Fetur ya Laƙume kudaden da ya kamata ace sun baiwa Gwamnatin Tarayya a Matsayin harajin da ake bayarwa domin a rarraba duk ƙarshen wata.

“A cewar shi Kimanin N111,966,456,903.74 zasu cire daga abunda aka samu na riba daga watan April 2021 Oil and Gas wanda ya kamata a ce an sanya a Asusun Gwamnatin Tarayya domin watan May 2021.”

Takadar wadda aka rubuta April 26 zuwa ga Babban Akawun na ƙasa tace Kampanin na NNPC yasamu ƙaracin haraji ne na N111,966,456,903.74 a watan February dalilin yadda aka samu tataccen Man Fetur wanda zai zoma Najeriya akan kudi N184 duk lita ɗaya maimakon N128 duk lita kamar yadda aka saba

Ya kuma danganta haka da rashin samun Matsaya akan farashin Man Fetur din tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƴan Kungiyar ƙwadago

Tunda farko dai Kyari ya bayyana cewa Kampanin bazai cigaba da iya daukar Nauyin biyan tallafin Man Fetur ba inada ya bayyana cewa farashin Man Fetur zai iya kasancewa tsakanin N211 zuwa N234 kowace litre.

Haka yake nufin cewa masu Amfani da Man Fetur basu biyan ainahin farashin Man wani ne a wani wuri yake cika masu cewa Mr Kyari.

Dama dai ƙasar nan tana dogara ne da harajin Kampanin Man Fetur na NNPC wajen samu Kudaden shigar ta sai kuma Harajin da ake kar’ba daga Kampanoni na Ƴan kasuwa da kuma Hukumar tattara haraji ta ƙasa.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: