Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Kwankwaso, har yanzu kafafunsa na hannun hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) biyo bayan tsare shi da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi a ranar Asabar, wata majiya ta sanar da jaridar PlatinumPost.

Hukumar EFCC tana yiwa jigo na jam’iyyar PDP tambayoyi kan zargin zamba cikin kudin ‘yan fansho.

Majiyar ta tabbatar da cewa tsohon gwamnan yana amsa tambayoyi kan zargin zamba, a don haka ko dai a bada shi beli ko kuma a gurfanar da shi gaban wata kotun da ta cancanta a ranar Litinin.

A daya daga cikin irin wannan korafe-korafen, ana zargin tsohon gwamnan da karkatar da kudin ‘yan fansho Naira biliyan 10 wanda ya gina gidaje amma a baya ya musanta wannan zargin.

PlatinumPost ta tattaro cewa Kwankwaso, wanda shima tsohon Sanata ne, yana cikin matsala kan zargin karkatar da kudaden kananan hukumomi na biliyoyin nairori.

A cikin takardar koke, wacce Barista Mustapha Danjuma, ya rubuta a madadin Injiniya Abubakar Maisha’ani da Alhaji Najumai Garba Kobo, ya yi zargin cewa Kwankwaso ya karbi gudunmawar Naira miliyan 70 daga kowace karamar hukuma 44 na jihar Kano (jimillar kudi Naira biliyan uku da miliyan dari takwas) wanda yayi takara da su a zaben fidda gwani na shugaban kasa a 2015.

Kwankwaso ya tsaya takarar fidda gwani na shugaban kasa a APC a 2015 amma ya sha kaye a hannun shugaba Muhammadu Buhari.

Daga baya ya koma jam’iyyar (PDP), inda aka ce yana kallon tikitin takarar shugaban kasa na 2023 na jam’iyyar.

Mun yi Kokarin jin ta bakin kakakin hukumar EFCC kan cigaba da tsare jagoran tafiyar Kwankwasiyya, anma hakan ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here