kungiyar horas da manyan ma’aikatan gwamnati wato ” National Institute for Policy and Strategic Studies da ke Kuru a Jos ta shirya taron cin abincin dare don karrama wadanda suka halarci bada horo na cibiyar karo na 44 da suka kawo ziyarar rangadi a Katsina.

Ziyarar rangadin na cikin abubuwan da ake bukata don cika sharuddan samun lambar karramawar ta MNI a cibiyar.

Kuma abinda suka yi nazari shi ne inganta mulkin K/Hs a Najeriya.

Da yake magana a wurin cin abincin daren, Kanwan Katsina hakimin Ketare Usman Bello Kankara ya yanke shawarar ganin an inganta mulkin kananan hukumomi don bunkasa harkokinsu da cin gashin kai.

Usman Bello Kankara wanda shima memba ne a kungiyar tsaffin daliban cibiyar ta horas da manyan jami’an gwamnatin a karo na 34, ya ce akwai bukatar samar da daidaito a tsarin aikin gwamnati na kananan hukumomi don ganin sun ci gaba.

Kanwan Katsina ya yi nuni da cewa akwai bukatar a bunkasa hanyar samun kudin kananan hukumomi don rage dogaro kaco kam kan daunin gwamnatin tarayya.

Basaraken wanda ba bayyana mahimmancin horas da ma’aiktan kananan hukumomi da sake horas da su, ya bada shawarar a kara inganta tsarin hukunci da kuma na bada lada ga ma’aikatan don auna kwazansu.

Sauran da suka yi magana a wurin cin abincin daren sun hada da shugaban kungiyar tsaffin daliban cibiyar Lawal Aliyu Daura, da mataimakin babban sufeton yan sandan Najeriya AIG Danlami Yar’adua, da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here