Gwamnan jihar Katsina ya bayyana bukatar ganin an yi bitar tsarin daunin kudaden da ake ba kananan hukumomi daga gwamnatin tarayya a cikin kasar nan.

Aminu Bello Masari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya amshi bakuncin wadanda suka halarci wani horo akan zartarwa karo na 44 a wata cibiya mai suna” National Institute for Policy and Strategic Studies Kuru karkashin jagorancin daraktan bincike na cibiyar a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Ya ce, yima tsarin mulkin kananan hukumomi dauka daya ba tare da la’akari da banbancinsu ba, shi ne ya taimaka wurin samun matsalolin da wasu kananan hukumomi ke fama da su.

Gwamnan ya ce a daidai lokacin da wasu kananan hukumomin keda hanyoyin samun kudin shiga, wasu sun dogara ne kacokam kan daunin da gwamnatin tarayya ke basu.

Ya ce irin wannan kananan hukumomin da ke cikin irin wannan mawuyacin halin basu iya gudanar ayyukan ci gaban kasa, baya ga biyan albashi.

Saboda haka yake yin kira da a yi bitar tsarin don ganin an magance matsalar.

Saidai gwamnan ya yaba ma shugaban kasa Muhammad Buhari bisa bullowa da sharye sharyen tallafawa rayuwar al’umma don ganin an taimaka wa magidanta, mata, da dama matasa.

Tunda farko, saida shugaban tawagar wanda kuma shi ne daraktan bincike na cibiyar Professor Dumpamsha ya ce ziyarar zuwa jihar na cikin rangadin nazarin da suke yi don gudanar da binciken halin da kananan hukumomi suke ciki, da kuma ganin irin wahalhalun da al’ummominsu ke sha.

Professor Dumpamshai ya kuma koka kan irin matsaolin da jihar nan ke fama da su, wanda ya hana ta ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here