Akwai Buƙatar A Yiwa Buhari Gwajin Lafiyar Ƙwaƙwalwa- Oby Ezekwesili

Akwai buƙatar ayiwa Buhari gwajin ƙwaƙwalwa

Akwai Buƙatar A Yiwa Buhari Gwajin Lafiyar Ƙwaƙwalwa- Oby Ezekwesili

Tsohuwar Ministar Ilimi, Oby Ezekwesili wadda kuma tana gaba-gaba wajan caccakar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa, ya kamata a yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari gwajin ƙwaƙwalwa.

A ka’ida majalisar tarayya ce ke neman irin wannan gwaji idan ana tunanin shugaban ƙasa ya gaza ko kuma yana fama da wani rauni, kamar yanda kundin tsarin mulki ya tanada.

Amma Oby Ezekwesili tace a matsayin ta na ƴar ƙasa da sauran ƴan Najeriya, zasu nemi Likitoci masu zaman kansu suwa shugaban kasar gwajin ƙwaƙwalwa da kuma na jiki dan tantance ko zai iya cigaba da shugabanci ko kuwa a’a.

Tace hakan ya zama dole saboda yanda al’amura ke cigaba da taɓarɓarewa a ƙasarnan ba tare da ɗaukar mataki ba. Tace a matsayinta na ƴar ƙasa mai kishin jama’arta, ba zata taɓa bari al’amura su cigaba da tafiya a haka ba tare da yin wani abu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here