Advert
Home Sashen Hausa Akaran farko dakarun sojojin Nijeriya zasu fara Amfani da Robots domin yakar...

Akaran farko dakarun sojojin Nijeriya zasu fara Amfani da Robots domin yakar ta,addanci a fadin Nijeriya baki daya.

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Akaran farko dakarun sojojin Nijeriya zasu fara Amfani da Robots domin yakar ta,addanci a fadin Nijeriya baki daya.

Dakarun sojojin Nijeriya na shirin kirkiro na’urorin da zata taimaka masu wajen yakar matsalar rashin tsaron Nijeriya.

Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa Hukumomin NITDA da NCAIR ne za su taimakawa jami’an sojojin Nijeriya wajen cin ma wannan burin na su na kirkirar mutum mutumi watau Robots

Shugaban NACEST, Janar Yahaya H Abdulhamid ne ya kai wa shugaban NCAIR ziyara a kan batun.

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa sojojin Nijeriya na kokarin komawa amfani da mutum mutumi watau Robots da sauran na’urorin kimiyya da fasaha wajen magance rashin tsaron Nijeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hukumar NITDA da NCAIR za su hada-kai domin kirkiro sababbin hanyoyin da za a shawo kan matsalar tsaron da ya addabi Nijeriya.

Wadannan hukumomi da ke kawo cigaba ta fuskar fasahar IT da kuma kirkire-kirkiren mutum mutumi za su bada gudumuwa wajen kawo zaman lafiya a cikin Nijeriya.

Rahotannin da muka samu yanuna cewa wannan yunkuri da za a yi zai taimaka sosai wajen samar da bayanan da suka danganci sha’anin tsaro ta hanyar cin moriyar fasahar zamani.

A jawabin da Isa ya fitar, yace za su hada-kai da sojoji domin kirkiro na’urorin da za su yaki miyagun mutane a cikin Nijeriya.

Shugaban hukumar yace an kafa NCAIR ne domin bincike da kirkiren zamani, tana yin aiki ne fasahar AI, mutum mutumi da IOT, da sauran cigaba na Duniya.

Jaridar Sahara Reporters tace za a tura wadannan robots masu kama da mutane zuwa filin yaki domin su kawo karshen ‘yan ta’adda, da duk wasu miyagun ‘yan bindiga a cikin Nijeriya.

NCAIR na kokarin samar da kirkire-kirkire, salon kasuwancin zamani, samar da aikin yi, da kawo cigaban kasa.

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa da yiwuwar duba samar da bam na komguta da zai yi aiki da fasahar WLAN a fagen fama.

Muna rokon ubangiji Allah ya azurta kasar mu Nijeriya da zaman lafiya

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...