Advert
Home Sashen Hausa Akan shinkafa; Jami'an Kwastam sun kashe fiye da mutum goma a Katsian

Akan shinkafa; Jami’an Kwastam sun kashe fiye da mutum goma a Katsian

 Jami’an Kwastom Sun Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Akalla 15 Da Raunata 20 A Jibia Jahar Katsina

Daga Wakilinmu

Da safiyar yau litinin 9 ga watan Ogustan 2021, jami’an hukumar kwastom suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15, yayin da mutane akalla 20 suka ji rauni, a garin jibia dake karamar hukumar jibia ta jihar katsina.

Majiyarmu ta shaida mana cewa lamarin ya faru biyo bayan artabo a tsakanin jami’an hukumar fasa kauri da wani mutum dan kasuwa, wanda ya dauko buhun shinkafa 1 akan babur daga garin jibia zuwa kauyensa “faru” dake akan titin zamfara.

Wani mazaunin garin, ya sanar damu cewa “Jami’an na Kwastom sun bi mutumin da niyyar su kama shi, amma hakan yayi sanadiyyar suka banke shi ya mutu, da wasu mutane akalla 15 wandanda basu ji basu gani ba, masu sana’o’i a bakin titi, tare da raunata wasu wadanda suka kai kimanin mutune 20.”

Yanzu haka dai wadanda suka jikkita, an garzaya dasu zuwa babbar asibin General dake garin na Jibia domin a duba lafiyarsu.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Alleged Defamation: Gov. Masari demands N10bn, apology from journalists

Gov. Aminu Masari of Katsina State has demanded the payment of N10 billion as damages from Mr. Emmanuel Ogbeche and Mr. Ochaika Ugwu, Chairman...

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina…..

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina..... A ranar Alhamis...

DIRECTOR-GENERAL INAUGURATES NYSC MEGA PRINTING PRESS

NYSC Director-General, Major General Shuaibu lbrahim today inaugurated the NYSC Mega Printing Press in Kaduna. He said the project, which was conceived almost a decade...

Shugaba Buhari Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Iyayen Hanifa, Yarinyar Da Aka Kashe A Kano.

Daga Zaharaddeen Gandu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa 'yan sandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai...