An Bukaci Hukumomin Tsaron Najeriya Da Su Kama Ministan Yada Labarai Lai Muhammad Saboda Kare ‘Yan Bindiga.

Kungiyar Marubutan Kare Hakkin Dan Adam ta Najeriya, HURIWA, ta tuhumi hukumomin tsaro da su kamo tare da gurfanar da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed saboda zarginsa na kare makiyaya masu aikata laifuka.

HURIWA ta yi wannan kiran ne a ranar Talata ta wata sanarwa da mai kula da ayyukan ta na kasa, Emmanuel Onwubiko ya fitar.

Wannan martani ne ga furucin da Ministan ya yi cewa ‘yan bindiga ba kamar masu son ballewa ba ne, saboda su ‘yan bindigar ba sa son haifar da rarrabuwa a kasar.

HURIWA, a cikin sanarwar ta, ta ce, “Neman kariya ga masu aikata laifi ‘yan ta’adda ya sabawa dokar Najeriya mai yaki da ta’addanci wanda ministan yada labarai ya karyata tare da yin watsi da ita.

Kungiyar tace, “Karewar da Lai Mohammed yayi ma ‘yan bindiga masu dauke da makamai ya tabbatar da cewa akwai wata manufa a hukumance a Aso-Rock ta tallatawa da daukar nauyin hare-haren ta’addanci da ke kara yawaita a duk fadin kasar da aka fi kaiwa Kiristoci ko wadanda ba Fulani ba, irin su Hausawa manoma a Arewa maso Yamma.

Ta ƙara da cewa: “Hare -haren ta’addanci da ‘yan ta’adda na Fulani suka kai a kasuwar Goronyo a Sokoto sun nuna cewa watakila sojoji ne ke yaudarar ‘yan Najeriya wadanda ke ci gaba da fitar da labaran farfagandar ‘yan jarida da ke ikirarin sojin sun kashe wasu adadi na ‘yan ta’addan Fulani a kewayen jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

“Yanzu hirar da Lai Mohammed ya yi ta kara tabbatar da tuhumar da miliyoyin ‘yan Najeriya ke yi cewa Gwamnatin Tarayya tana ba masu goyon bayan ‘yan ta’adda dama a cikin gwamnati,” Inji Kungiyar.

Jaridar Sokoto

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here