A jiya wasu musulmi daga yankin katsina sun gudanar da faretin murnar maulud a garin na katsina musamman cikin birni in watan maulud ya kai Goma sha biyu.
Al’umar musulmi idan watan ya kama kulum cikin tarurruka suke tun daga Makarantu, Zawiyoyi, da kuma Al majiran manyan malamai.
Jiya al majiran Malam yakubu yahaya katsina ne shugaban yan uwa na jahar katsina, suka gudanar da bukukuwan,Yau kuma makarantar sheikh Malam Iyal gafai ke yin nasu, Indaza a kwana ana karatu, ranar lahadi kuma mahardatan Ishiriniya zasuyi nasu haka dai lungu da sakon garin yake kasancewa har watan ya shige.