Advert
Home Sashen Hausa AIKIN HANYOYIN CIKIN GARIN MALUMFASHI DA FUNTUA DA SANATA BELLO MANDIYA ZAIYI.

AIKIN HANYOYIN CIKIN GARIN MALUMFASHI DA FUNTUA DA SANATA BELLO MANDIYA ZAIYI.

A yau Litinin 8/11/2021 Sanata Mai Wakiltar Shiyyar Funtua, Malam Bello Mandiya zai fara Gudanar da aikin wasu tituna na Kananan hukumomin Malumfashi da Funtua.

A karamar Hukumar Malumfashi Za’ayi hanyoyi kamar haka.

Hanyar da ta tashi daga kantsauni tabi ta makabarta zuwa bye pass.

Hanyar Layin ‘yan goro daga Kofar Gidan Marigayi Alh Ladan Ami zuwa titin layin lamarudu.

Hanyar Amada Gangarawa tabi ta Kofar Gidan Marigayi Alh Bube zuwa Kofar Gidan Alh Na Tudu.

Hanyar Kofar Gidan Marigayi A.N.G zuwa titin stadium, tabi ta Kofar Gidan Alh Zilkifilun ta had’u da babban titin Express na Unguwar Sodangi.

Hanyar da ta tashi daga titin BCJA, tabi ta Kofar Gidan Galadiman Daji/Nuhu Nepa ta hau tudun Mishau zuwa titin kwandala.

Hanyar daga titin kwandala tabi ta Kofar Gidan Danmaliki ta shiga ( Water Board Quarter’s) zuwa Unguwar Mata ta jikin gidan Danyari ta tabi ta Kofar Gidan Alh Usaini Mahuta ta ‘bulla babban titin Express na MTD police station.

Hanyar da ta tashi daga BCJA zuwa Kamfanin Gurza.

Akwai na cikin garin Funtua da zan kawo Insha Allahu.

Wad’annan hotunan aikin fitila mai amfani da asken rana ne da Sanata Bello Mandiya yake Gudanarwa a karamar Hukumar Malumfashi da sauran Kananan hukumomin na shiyyar Funtua.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...