afuwan ƴan Najeriya kan rashin wuta

wuta

Ministan lantarki Injiya Sale Mamman ya nemi afuwan ƴan Najeriya kan rashin samun wuta yana mai cewa nan bada jimawa ba komai zai gyaru.

Ministan ya alaƙanta rashin wutar da ake fama da matsalolin da ake fuskanta a cibiyoyin tura wutar lantarki guda 8 na ƙasar.

Sannan ya ce an rufe cibiyar wuta ta Jebba domin yin wasu gyare-gyare da akan yi kowacce shekara.

Haka zalika ya bayyana wasu ciboyoyi 7 da suka hada da Geregu da Sapele da Omotosho da Gbarain da Omuku da Paras da Alaoji da ya ce suna fama da ƙarancin iskar gas, yayinda da tashar samar da wuta daga ruwa ta Shiroro na buƙatar gyara.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here