ANKASHE WANI GAWURTACCEN ƊAN FASHI DA MAKAMI A ƘARAMAR HUKUMAR BAKORI TA JIHAR KATSINA
Ƴan fashi da makami suka tare hanyar Bakori – Kabomo, jihar Katsina. DPOn Bakori ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa wurin, a take aka fara musayar wuta kuma a sakamakon haka ne aka kashe daya daga cikin ‘yan fashin dake da bindiga kirar gida sauran suka tarwatse watse.
Kakakin Rundunar Yansandan jihar katsina Gambo Isah ne ya sanar da hakan kuma yace ana cigaba da farautar sauran abokan ta’addaancin nasu inda suka zubar da wasu makaman suka gudu