ADALCI KUKE SO KO GOYON BAYAN MAHADI

Jamilu hassan Dutsinma

A labarin da muke samu yanzu da daren nan cewar gobe Alhamis 03-12-2020 wata ƙungiya za ta kira taron manema labarai kan nuna goyon bayan su a kan Mahadi Shehu, wanda ya yi shura wajen cin mutuncin manyan mutane a jahar Katsina. Ya kuma zubar da mutuncin jahar katsina a idon duniya

Cikin irin mutanen da Mahadi shehu ya riƙa ci wa mutunci har da mai martaba sarkin Katsina da Daura, don kuwa Gwamanan jahar Katsina da ma jami’an Gwamnatin ya maida su wasu ƙaskantattun mutane saboda sharri irin na gidan duniya babu wanda Mahadi Shehu bai yi masu ba. Ya yi masu sharri, ƙazafi, ƙarya da cin mutunci.

Wannan kungiyar a bisa labarin da mu ke samu kun ce za ku nuna goyon bayan ku a kan Mahadi Shehu, na kamu, ko gayyatar da jami’an ‘yan sanda su kayi masa, wanda a cikin abinda za ku yi ma manema labarai bayani har da iƙirarin tafiya kotu kan ana bincike tare da tuhumar Mahadi Shehu da jami’an ‘yan sanda su ke gudanarwa a kai.

ABIN TAMBAYATA ANAN SHI NE :

Shin lokacin da Mahadi Shehu yake cin mutuncin masu mutunci babu ƙungiyar ku ne?

Me yasa duk ƙarya da ƙazafin da ya ke yi ma jami’an Gwamnatin jahar Katsina su ba ku tsaya masu akan ya daina aibata su ba?

Shin mutuncin da ya zubar ma gidajen sarautar Katsina da Daura ya tashi a banza kenan?

Ko kuwa kuna son ku nuna ma duniya kuna goyon bayan cin mutuncin da Mahadi Shehu ya ke ma mutane? Da zubar da mutuncin katsina

Muna Jan hankalin ku da ku bar jami’an ‘yan sanda su gama gudanar da binciken su a kan Malam Mahadi Shehu, saboda dokar ƙasa ta basu dama a kan hakan.

Ko kuwa kuna son ku nuna ma duniya za kuyi ma dokokin ‘yan Sanda da na shari’a karan-tsaye ne?

Mahadi Shehu shi ne ya ke rokon a kai shi kotu, sai kuma wasu daga cikin waɗanda yake ma sharri da ƙarya tare da ƙazafi su ka ba Hukumar ‘yan Sanda wasu bayanai akan karairayin da yake masu don ɗaukar matakin shari’a.

Shin ƙungiyar ku so ta yi a hada Mahadi Shehu da ‘yan daba ne maimakon jami’an ‘yan sanda?

Wadannan tambayoyin na tabbata duk mai hankali kuma mai son ayi aiki da doka da oda, amsar da zai bada a kan su, su ne a bari doka tayi aiki akan duk wani ɗan ƙasa da ake tuhuma.

Idan kuma ƙungiyar ta ki bari to, ta tabbata suna goyon bayan cin mutuncin da Mahadi Shehu ke yi ma bayin Allah’n da, ba su ji ba, ba su gani ba.

Jamilu Hassan Dutsin-ma
02-12-2020
08037392680

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here