Idan Allah Ya kai mu cikin watanni ukku na farkon shekarar 2022 mai kamawa za a gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar Katsina.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa ta musamman da yayi da manema labarai yau a fadar Gwamnatin Jiha dake nan birnin Katsina.

Gwamnan ya kara da cewa duk da cewa kananan hukumomi da yawa har yanzu basu iya biyan kawunan su albashi, hakan ba shi ya hana a gudanar da zabukan ba, illa dai kararrakin da jam’iyyar PDP tayi ta kaiwa a kotuna daban daban kan kada a bar gwamnati tayi zabukan.

Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa sama da kashi saba’in (70%) na abinda ake bukata na kayan zaben yana kasa, kuma in Allah Yaso nan ba da jimawa ba sauran za su kammala.

Ta bangaren tsaro kuwa, duk da cewa ana samun ci gaba ta bangaren raguwar hare hare da asarar rayuka, Gwamnan ya kara nanata kiran da yayi, na al’umma mu kare kawunan mu daga ‘yan ta’adda. Ya nuna cewa akwai ganganci ga al’umma sama da Miliyan Takwas su zura ma ‘yan sanda dubu ukku su basu tsaro. Sai yayi kira ga al’umma da su tabbatar da duk makamin da za su mallaka to ayi mashi rajista da hukuma. Kuma gwamnati a shirye take ta taimaka ma al’umma kan hakan. Amma ba za a lamunci wasu su bar garin su ba zuwa wani gari da sunan sa kai, kowanne shuwagabannin al’umma su tsara kuma su tsare yadda za su gudanar da wannan aiki ba tare da saba dokar kasa ba.

Ya kuma kara da cewa, da yardar Allah, Gwamnati mai shigowa ba za ta gaji wannan matsalar ta tsaro ba.

Da aka tambaye shi maganar shari’ar da PDP ta kai kuwa, in da suke inkarin maganar da yayi ta cewa an kori karar da suka shigar, Gwamnan ya ce ai sun kai karar a maida su ne, kotu kuma bata ce a maida sun ba, sai dai tace a biya su kudade, tuni kuma an gama biyan su. Maganar kuma biyan Sakatarori da Kansilolin nadi (Supervisory Councilors), Gwamna Masari ya ce ai ba zabar su aka yi ba.

A karshe, Gwamna Aminu Bello Masari yayi kira ga al’ummar jihar nan da ma na kasa baki daya, da muci gaba da addu’o’in Allah Ya shiga cikin al’amurran mu Ya sama mana mafita. Domin dorewa da kuma cigaban kasar sune jigon gina al’ummar da za ayi alfahari da ita nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here