An sace ‘mata 50’ a Katsina cikin kwana biyu

Rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata kimanin 30 daga wani kauye a kudancin jihar da tsakar daren jiya.

Hakan ya zo ne bayan da wasu bayanan kuma suka ce maharan sun sace wasu matan fiye da 20 daga wasu kauyukkan biyu a shekaran jiya ranar Lahadi.

Sai dai jami’an tsaro a jihar ba su tabbatar da faruwar lamuran ba kawo yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here