Black Friday: Abubuwan da suka kamata ku sani game da ranar Black Friday

Ana karya farashin kayayyaki a lokacin Black

Hukumar ta ce ta hana yin amfani da kalmar Black Friday ce saboda, a cewarta tana nufin ‘bakar rana’ abin da bai dace da suna na rana mai girma irin ta ba.

A tattaunwarsa da BBC, Babban Kwamandan hukumar Sheikh Harun Ibn Sina, ya ce: “Abubuwa uku ne suka sa muka dauki wannan mataki: na farko ita kanta ranar inda aka kira ta ‘bakar Juma’a’ domin mu a Musulunci ita ce mafi alheri kamar yadda Annabi SAW ya bayyana.”

Sai dai wannan kalami ya sa ‘yan kasar da dama, ciki har da Musulmi suna sukar hukumar ta Hisba, inda suke bayyana ta a matsayin wadda ta jahilci ma’anar ‘Black Friday’.

Mun yi nazari kan asalin Black Friday da ma’anarta da ma amfaninta.

Mana’ar Black Friday

Bayanan bidiyo,Bidiyon da ke bayani kan yadda za a rage radadin koma bayan tattalin arziki

Black Friday wani suna ne da ake kiran Juma’ar da ta biyo bayan ranar Alhamis din da ake bikin cika-ciki a Amurka, bikin da ake yi a ranar Alhamis ta hudu a ko wane watan Nuwamba na ko wacce shekara.

Juma’ar da ta biyo bayan ranar cika-cikin ake dauka a matsayin lokacin fara sayayyar kirsimeti a Amurka, kuma an fara hakan ne tun daga shekarar 1952.

An kwashe shekara da shekaru ana amfani da Kalmar Black Friday, kuma wata rana ce da manyan ‘yan kasuwa ke amfani da ita domin tallata kayayyakinsu da suka yi ragowa a kasuwa, kafin a tafi hutun karshen shekara.

Da yawan kantuna suna karya kayayyakinsu a ranar da ake kira Black Friday tun cikin daren Juma’ar, wasu ma suna farawa ne tun a ranar Alhamis din cika-ciki, domin kada a bar su a baya.

Black Friday ba ranar hutu ba ce, kamar yadda wasu ke zato, sai dai wasu kasashen na ba da hutu ga ma’aikatansu domin samun damar yin sayayya a ranar.

Wasu wuraren na ba da hutu narar Juma’a ga Alhamis din da ta gaba ce ta sai kuma Asabar da Lahadi sai ya zama an samu hutun kwana hudu a jere a Amurka.

Black Friday daya ce daga cikin ranakun da aka fi yin ciniki a cikinsu a duniya, tun daga 2005, wanda wannan ke nuna yadda take da tasiri kan tattalin arziki a karshen shekara.

Amfanin ranar Black Friday

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa babban amfanin ranar Black Friday shi ne yadda masu yin sayayya skan sayi kaya cikin rahusa.

Don haka ne ma mutane da dama suke jira sai lokacin Black Friday kafin su sayi wasu kayayyaki saboda ana zaftare farashinsu, a cewar masana tattalin arziki.

A halin da kasa irin Najeriya ta tsinci kanta a ciki musamman bayan fuskantar koma bayan tattalin arziki mafi girma cikin shekaru 30, masana na ganin samun kaya cikin rahusa zai taimaka wa ‘yan kasar wajen samun sassuci a game da rayuwarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here