Za’asake gina masallatan da aka lalata a Enugu
Gwamnan jihar Enugu a kudancin Najeriya Ifeanyi Ugwuanyi, ya bayar da umarnin sake gina wasu masallatai biyu da aka lalata a jihar.
Wasu masu zanga-zanga ne suka lalata masallatan na garin Nsukka a jihar da mabiya addinin Kirista ne suka fi yawa.
Shugaban ƙaramar hukumar Nsukka, Mr. Cosmas Ugwueze ne ya bayyana batun gyaran a lokacin da ya ziyarci masallatan da aka lalata ɗin a madadin gwamnan jihar.

Hukunci ga mai fyaɗe a Kano
Kungiyoyin kare hakkin mata a Kano, sun yi na’am da hukuncin da wata Babbar Kotun Tarayya da ke jihar ta yi wa wani mutum mai shekara 42 na ɗaurin shekara bakwai a gidan yari da biyan tarar naira miliyan guda saboda samunsa da laifin lalata wata yarinya budurwa.
Kungiyoyin dai sun ce duk da cewar hukucin ba zai goge irin raɗaɗin da ke zuciyar iyaye da ita wadda aka ci wa zarafin ba amma dai hakan zai yi tasiri wajen zaman izina ga masu aikata irin wannan laifi.
A ranar Talata ne kotun ta ce ta samu mutumin mai suna Salisu Tanko da laifin cin zarafi da lalata wanda ya saɓa wa sashe na 16 na dokar hana safarar bil’adama ta shekara ta 2015.
Rahotannin kafafen yada labarai sun ambato lauya mai shigar da kara Abdullahi Babale na shaida wa kotun cewa wani lokaci a wata Janairun wannan shekarar ne, wanda ake ƙarar ya kai yarinyar wani kangon gida ya biya ta naira 500 kana ya yi lalata da ita.
Wanda ake ƙarar dai bai musanta laifin ba, abin da ya sa alƙalin ƙotun Mai Shari’a Sa’adatu Ibrahim Mark ta yanke masa hukunci ɗaurin shekara bakwai a gidan yari da kuma tarar naira miliyan ɗaya.
Ta ce za a ƙara wa mutumin wata shekara daya idan ya kasa biyan tarar. Hukumar yaƙi da safarar bil’adama ta NAPTIP da ita ce ta shigar da ƙarar a gaban kotun.

Kotu ta riƙe Naziru Sarkin Waƙa

ASALIN HOTON,SARKIN WAKA INSTAGRAM
A ranar Laraba ne wata kotu a Kano ta soke belin da aka bai wa fitaccen mawaƙin nan Naziru Ahmed Sarkin Waƙa, inda ta gindaya wasu sababbin sharuɗɗan belin.
Sai dai kotun ta riƙe Naziru inda ta aike shi gidan yari saboda rashin cika sharuɗɗan a kan lokaci, duk da cewa an gindaya sharaɗɗun ne a ranar Larabar.
Ana ƙarar Naziru ne dai kan cewa ya saki wata waƙa ba tare da hukumar tace fina-finai ta Kano ta tantance ba.
Sharuɗɗan sun haɗa da cewa sai ya kawo wani Maigari da zai tsaya masa da kuma Kwamandan Hizbah na ƙaramar hukuma a matsayin sharuɗɗan beli.
Wani makunsancinsa ya ce sun cika sharuɗɗan, sai dai kuma ba a samu kai wa ga alƙalin da zai bayar da umarnin ba da belin ba.
A watan Satumban 2019 ne aka fara kama Naziru Sarkin Waƙa amma daga bisani kotun majistare da aka kai shi ta sake shi bayan ya cika sharudan belin da kotun ta yanka masa.

A Kamaru
A Kamaru kuwa, wasu mutane ne ɗauke da makamai suka yi kutse da safiyar yau Laraba a cikin makarantar Kulu Memorial College a birnin Limbe ta yankin renon Ingila, suka ƙona wasu azuzuwan karatu da ofisoshin makarantar, bayan sun zane wasu ɗalibai da malaman makarantar.
Wani bidiyo mai tsawon daƙiƙa 54 da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna irin ɓarnar da suka yi.
Wannan lamari ya auku ne kwana guda bayan sace wasu malamai 11 da aka yi a Makarantar Presbyterian ta birnin Kumbo.

Masu satar mutane sun kashe mai ciki a Kaduna
An yi jana’izar wata mata mai cikin wata biyu da masu satar mutane suka hallaka ta a Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Masu satar mutanen sun je gidanta ne da niyyar sace ta amma kuma sai suka harbe ta a cikinta inda hakan ya yi sanadinta.
Lamarin ya faru ne a yankin Rigachikun, wata unguwa da ke wajen gari a hanyar zuwa Zariya.
Matar dai ta mutu ta bar ƴaƴanta uku.

An ɗage dokar hana fita a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta ɗage dokar hana fita da ta sanya a makon da ya gabata a fadin jihar.
Gwamna Nasir El-Rufa’i ne ya sanar da hakan a ranar Laraba da yamma a shafinsa na Tuwita.
An sanya dokar hana fitar ne bayan da mutane suka dinga yi wa rumbunan ajiye abinci rufdugu suna kwasar kayayyakin da suka ce na tallafin kullen korona ne da gwamnatin tarayya ta bayar a ba su amma ba a raba ba, duk da cewa dai gwamnatocin jihohi sun musanta hakan.