Kakakin Majalisar dokokin Jihar Katsina ya faɗi hakan yau a lokacin da Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina kuma Dan takarar Gwamna a shekarar 2023 ya ziyarci Majalisar Dokokin Jihar Katsina yau talata 10/5/2022.

Alh Mannir Yakubu ya kai ziyarar a zauren Majalisar dokokin da niyyar sheda ma Shuwagabannin Majalisar tsayawa takarar shi, tare da neman goyon su ta kowacce fuska domin nasarar Jihar Katsina itace ƙudurin Mataimakin Gwamna Kuma itace kudirin Yan’majalissar.

Alh Mannir Yakubu ya bayyana ma zauren Majalisar ƙudurin shi na tsayawa takarar a shekarar 2023, tare da kudirin shi na ciyar da Jihar Katsina a gaba ta hanyar amfani da gogewa da masaniya da yake da ita ta dukkan ayyukan alherai da Gwamna Masari ya shimfida ma Jihar Katsina, tare da dasawa da cigaba da ayyukan alherai da Gwamna Masari ya Shimfiɗa ma Jihar Katsina.

Alh Mannir Yakubu bayyana cewa mulki ba wasa bane shiyasa tun farkon fara shirin kafa Gwamnatin APC aka sanya masana kowanne fanni suka gano matsalolin da fannonin daban daban ke buƙata, kuma da kafa Gwamnatin aka tun kari matsalolin domin magance su, wanda kawo yanzun cikin yardar Allah an magance wasu matsalolin da yawa, kama daga bangaren ilimi da lafiya da hanyoyin sufuri, da samar da ruwa tsaftatacce, da dai sauran su.

Tun farko shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina yace ya bayyana Alh Mannir Yakubu a matsayin mutumin kirki mai aƙida ta kirki da gaskiya da rikon amana kuma mai biyayya.

Shugaban Majalisar yace yadda biyayya tayi aiki a Jihar Kano Allah yasa tayi aiki a Jihar Katsina.

A nashi Jawabin Dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Katsina ta tsakiya Hon. Aliyu Abubakar Albaba ya bayyana Mataimakin Gwamnan a matsayin Dattijo adali sahihi kuma mutum nagari wanda duk al’ummar da ta samu irin shi a matsayin shugaba ta samu babban alheri.

Wasu daga cikin Yan’malissar Zartaswa da wasu daga cikin yan majalisar Dokoki sune suka rufa ma Mataimakin Gwamnan baya, Daga cikin su akwai mai baiwa Gwamnan Katsina shawara ɓangaren harkokin noma da albarkatun kasa kuma Shugaban yakin neman zaben Mataimakin Gwamnan Dr. Abba Yakubu Abdullahi, da Shugaban Hukumar bunkasa matsakaita da ƙananun masana’antu ta Jihar Katsina (DG KIPA) Alh Ibrahim Tukur Jikamshi wanda shine Sakataren kwamitin yakin neman zaɓen Mataimakin Gwamnan, da dai sauran al’ummomi yan kasuwa da yan siyasa da Jami’an Gwamnati, da abokai da yan’uwa da aminan arziƙi da dai sauran su.

Muhammad Barmo Hadimi Na Musamman Ga Mataimakin Gwamna Bangaren Sabbin Kafafen Sadarwa (New Media) 10/5/2023

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here