Advert
Home Sashen Hausa ABINDA NA FAƊAWA WANDA SUKAI GARKUWA DANI SUKA FASHE DA KUKA.

ABINDA NA FAƊAWA WANDA SUKAI GARKUWA DANI SUKA FASHE DA KUKA.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Neja da ke arewacin Alhaji Muhammad Sani Idris ya ce nasihar da ya yi wa mutanen da suka yi garkuwa da shi ta sa sun rika zubar da hawaye.

Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da BBC Hausa bayan ya kubuta daga hannun ‘yan bindigar.

A cewar “daga karshe da za mu rabu na ce don Allah su ba ni dama na yi musu bayani. Na ce da sun san yadda saduwarsu da Allah za ta kasance, ni na tabbatar ba za su yi [garkuwa da mutane] ba… Ina wannan maganar yawancinsu suka fashe da kuka.”

Ya kara da cewa ko da yake sun nemi ya bayar da kudin fansa da suka kai mnaira miliyan 200 amma ya gaya mus ba shi da wadannan makudan kudi.

Sai dai ya ce sun daure hannaye da kafarsa tsawon kwana biyu suka kuma hana shi abinci.

– @bbchausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: