WANI AL’AMARI MAI BAN MAMAKI:- Antono wani mutum a ƙabari yana Numfashi bauan shekara guda da Bizne shi.
mai ban mamaki ya faru a jihar Imo, inda aka ga gawa tana numfashi – Kamar yadda bidiyon ya bayyana, gawar da ta shekara 1 a kwance aka gani tana numfashi – An ga yadda kwari suka fara cin akwatin gawar, amma jikin mamacin bai rube ba Wani al’amari mai firgitarwa ya faru a Umuoji, Amucha da ke jihar Imo, inda aka ga wani mutum da ya rasu shekarar da ta gabata yana numfashi.
Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, a bidiyon, mutane sun taru a kan akwatin gawa, inda aka ga mutumin yana numfashi. Mutanen sun yi ta ihu suna cewa “yana numfashi, yana numfashi” cike da mamaki. Kamar yadda labarin yazo, mutumin ya mutu ne ranar 9 ga watan Nuwamba, 2019 kuma an rufeshi ranar 8 ga watan Oktoban 2020, kamar yadda aka ji wani yana fadi a bidiyon.
An ji muryar wani mutum yana cewa, “mutumin nan ya mutu a shekarar da ta gabata da sati 3 kenan da birne shi, sai ga shi yana numfashi.”