Rundunar soji ta gargadi Sheikh Ahmad Gumi a kan kalamansa ga ƴan bindiga

Gumi da Attahiru

Rundunar sojin Najeriya ta gargadi babban malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ahmad Gumi da cewa ya iya bakinsa kan irin kalaman da yake yi a lokacin ziyarar da yake kai wa sansanonin ƴan bindiga a wasu sassan ƙasar.

Wata sanarwa da daraktan sashen watsa labarai na rundunar Birgediya Janar Mohammed Yerima ya fitar a ranar Talata da maraice ta ce, a yayin da rundunar ba ta son samun wani saɓani tsakaninta da Sheikh Gumi, amma tana son bayyana cewa rundunar sojin Najeriya ba ta tura dakarunta bakin aiki kan bambancin addini.

Rundunar sojin ta yi wannan gargadi ne sakamakon wani bidiyo da ya yadu da ke nuna Sheikh Gumi a wata ziyara da ya kai wa ƴan bindiga a cikin daji, yana ce musu yawancin sojojin da ke kai musu hare-hare ba Musulmai ba ne.

Sai dai Sheikh Gumi ya ce rundunar sojin ba ta fahimce shi ba ne.

“Don haka muna rokon Sheikh Ahmed Gumi da masu irin ra’ayinsa da su kame kansu kar su shigar da rundunar soji mai matuƙar ƙima cikin lamarin da zai zubar mata da daraja.

“Rundunar sojin Najeriya tana ci gaba da zama abar alfaharin ƙasar da kuma kare mutuncinta. Kalaman da za su ɓata ƙima da darajar rundunar sojin Najeriya ba rikici kawai za su jawo ba har husuma za su tayar a tsakanin ƴan Najeriya,” a cewar sanarwar.

Ta ƙara da cewa rundunar sojin na ayyukanta cikin taka tsan-tsan da bin dokokin da aka kafa ta a kai, da girmama haƙƙin ɗan adam ba tare da nuna wariya ba.

“Don haka babban abin kunya ne a ce wani malamin addini ya dinga ɓata ta da gangan a idon duniya.”

A ƙarshe sanarwar ta bai wa malaman addinin shawarar yin taka tsan-tsan a yayin da suke bayyana ra’ayoyinsu, da bai wa tsaron ƙasa muhimmanci, musamman a wannan lokaci mai tsanani da dakarun tsaro suke ƙara zage damtse don shawo kan matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

“Abin da dakarunmu ke bukata shi ne goyon bayan al’umma don yin aikinsu yadda ya dace,” kamar yadda sanarwar ta faɗa.

Wannan layi ne

Wane martani Sheikh Gumi ya mayar

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi ƙarin haske kan kalaman da ya yi bayan da rundunar sojin Najeriya ta gargaɗe shi kan abin da ta ce kalaman da ka iya ta da husuma.

Sai dai Sheikh Gumi ya ce rundunar sojin ba ta fahimce shi ba ne.

Ya ce batun da ya yi na cewa akwai bara-gurbi a rundunar, yana nufin a shekarun 2010 zuwa 2015 ne.

“Da nake magana kan matsalolin da ke rundunar sojin Najeriya, ina nufin lokacin shekarun 2010 zuwa 2015 ne, lokacin da wasu mutane da ke rike da madafun iko a rundunar suka bari mugayen abubuwa su kai ta faruwa.”

“A lokacin ne aka rika sa abubuwan fashewa har muka rasa wani babban Janar ɗin soja. Ni kaina na tsallake rijiya da baya da aka sa min abin fashewa,” ya shaida wa BBC.

Sheikh Gumi ya bayyana wa BBC cewa yana da kyakkyawar fahimta da rundunar sojin Najeriya kuma babu abin da ya sauya.

Wannan layi ne
Wannan layi ne

Me ya sa Sheikh Gumi zuwa wajen ƴan bindiga?

A farkon shekarar ne Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya fara shiga dazuzzukan da ƴan bindiga ke yin mafaka yana yi musu wa’azi da kira gare su su ajiye makamansu.

Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa ƙarancin ilimi na daga cikin matsalolin da ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a yankin arewacin Najeriya.

Wannan na daga cikin dalilin da malamin ya bayyana kan ƙaddamar da wani gangami na fita yankunan jihar Kaduna da ma wasu jihohin domin ilimantar da mazaunansu da kuma yi musu wa’azi.

Sai dai bayan da ya fadada shiga wurin nasu, a baya-bayan nan an ga wani bidiyo da yake ce musu dakarun sojin Najeriya da ba Musulmai ba ne suke kashe Fulani makiyaya, al’amarin da ƴan bindigar ke koka wa a kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here