Abin da ya sa na kama Bashir Ɗandago – Afakallah

SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya bayyana dalilin sa na cafke tare da gurfanar da fitaccen sha’iri Malam Bashir Ɗandago a kotu.

An dai kama mawaƙin ne yau a birnin Kano, aka gurfanar da shi gaban kotu mai lamba 58 da ke zaman ta a Nomansland, Kano, inda Mai Shari’a Aminu Gabari ya saurari ƙarar.

Bayan an gabatar da ƙarar, sai aka ɗage ci gaba da ƙarar zuwa gobe. Daga nan ‘yan sanda su ka wuce da Malam Bashir ofishin su inda za su tsare shi zuwa gobe lokacin da ake jin lauyan sa zai nema masa beli.

Afakallah ya bayyana wa mujallar Fim cewa ya sa an kama Ɗandago ne saboda ya karya dokar hukumar ta ƙin kai wata waƙa tasa a tace ta, ga shi kuma ta na ɗauke da ɓatanci kan wasu mutane.

Ya ce: “Gurfanarwar ta zo ne sakamakon waƙar da ya saka ba bisa ƙa’ida ba wanda a cikin waƙar ya ke ta maganganu da zage-zage.”

Afakallah ya ƙara da cewa: “Doka ce idan mutum ya yi waƙa dole ne ya kawo a tace. Don haka dole ne hukuma ta ɗauki matsayi kan wanda ya keta hukuma; duk wanda ya yi haka komai girman sa ba za a ga girman ba, haka kuma komai ƙanƙantar mai ƙanƙanta in dai ya cancanci haƙƙi za a ba shi haƙƙin sa, shi ma komai girman mai girma in dai ya taka doka dole  doka za ta taka shi.”

Shugaban ya ce, “A don haka yanzu mun gurfanar da shi a gaban kotu mai lamba 58 da ke zaman ta a Nomansland, Kano,  mun kuma yi iya namu sai kuma abin da kotu ta yanke.”

Da mujallar Fim ta tuna wa Afakallah cewar Malam Bashir ya na ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar mawaƙa masu yabon Manzon Allah (s.a.w.) na Jihar Kano waɗanda su ka taya hukumar wayar wa da mutane kai a lokacin da aka ce sai mawaƙan sun yi rajista da hukumar, don haka me ya sa ba a kira shi domin ja masa kunne ba, sai ya kada baki ya ce “Idan aka ce babba zai yi a kauda kai idan kuma ƙarami ya yi a yi masa hukunci, wannan shi ne rashin adalci.

“Ka ga shi ya kamata ma ya fi girmama doka kuma shi ya kamata idan ya taɓa doka doka ta fi aiki a kan sa domin a tabbatar da cewa da gaske ake ba wasa ake ba, ba wani ɗan bora ba wani ɗan mowa, magana ce ta duk wanda ya taɓa doka doka ta yi aiki a kan sa, don shi ne zaman lafiyar mu.

“In ban da doka ba yadda za a yi. Lokacin da ya fito ya na abubuwan sa ai shi ma haƙƙin wasu ya taka, a ce mutum ya fito ya na waƙa ya na zagin mutane da ashar a ce kuma wannan abin yabo ne, ka ga wannan bai kamata a ce babban mutum irin sa ya yi haka ba.”

A ƙarshe, Afakallah ya yi kakkausan jan hankali ga mawaƙa masu yabo kan dambarwar da ake yi tsakanin gwamnatin Jihar Kano da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da cewa, “Mu na kira da mawaƙa da su sani Kano gari ne na tarbiyya, gari ne na addini, gari ne na al’ada. Shi ya sa aka samar da Hukumar Tace Finafinai.

“Ba wanda zai zo ya yi mana ganin kan sa ta wajen keta al’adar mu ko addinin mu ko tarbiyyar mutanen mu. Wannan ko waye shi ya yi tsararo.

“Don haka maganar da mu ke ita ce lallai mawaƙa idan su na so su zauna lafiya a wannan jiha su bi ƙa’idojin Hukumar Tace Finafinai kuma shi ne zaman lafiyar su.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here