ABIN AL’AJABI: An Raba Tagwayen Mata Da A Ka Haifa A Manne A Asibitin Koyarwa Na Jami’ar Ilorin

Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH), Ilorin, Dake Jihar Kwara, a jiya ta yi nasarar raba tagwaye da ke hade da juna.

Asibitin ya gabatar da saitin tagwayen mata, wadanda suka hade a lokacin haihuwa, a raye ga jama’a bayan likitocin sun yi nasarar raba su.

Majiyoyi sun ce aikin da kungiyar likitocin ta yi duk da an yi shi cikin karancin kayan aiki a asibitin amma tayi Nasara.

Da yake jawabi ga manema labarai a Ilorin a jiya, Babban Daraktan Likita (CMD) na UITH, Farfesa Abdullah Yussuf, ya danganta wannan rawar da kwazo da jajircewa na mambobin kungiyar su 66 da aka samu A Matsayin Wani Jihadi domin kubutar da waɗannan Bayin Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here