TAKAITACCEN TARIHIN Hon. ABDULRASHID ABBA ALI.

An haifi Abdulrashid a ranar 22 ga watan Fabereru, 1973 a cikin Birnin Katsina daga cikin Iyalin Senator Abba Ali (Turakin Katsina). Ya yi karatunshi na allo a makarantar Marigayi Malam Uzairu domin samun Ilimi na addini a matakin farko don samun ingantattar rayuwa.

Ya yi karatunshi na firamare a makarantarKayalwa Primary School Katsina (watau Ahmadu Kumasi Science Model Primary School a yanzu), daga nan ya wuce zuwa Sekandaren Gwamnati ta Government College Katsina (GCK) a inda ya gama a shekara ta 1990. A shekara ta 2003 ya kammala Digirinshi na farko a fannin Kimiya watau B.Sc Physics a Jamiar Beyero da ke Kano (BUK). Ya yi Postgraduate Diploma in Education a 2007 a makarantar Fasaha ta
Hassan Usman Katsina. A shekara ta 2008 ya sake komawa Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) domin karin ilimi na gaba da digiri (Postgraduate Diploma) a bangaren Kimiyar Na’ura Mai Kwakwalwa (Computer Science). A shekara ta 2010, ya garzaya zuwa Kasar Malaysia inda yayi Digiri na Biyu akan Kimiyar Na’ura Mai Kwakwalwa Fannin Tsaro na Yanar Gizo (MSc Computer Science Information Security) daga Jami’ar Fasaha ta Kasar Maleysia (University of Technology Malaysia).

A fannin aikace-aikace daya gudanar, Abdulrashid Anba Ali ya fara aikin koyarwa a fitacciyar Makarantar Sakandare ta Kimiya ta Ulul-Albab (watau Ulul-Albab Science Secondary School Katsina). Daga bisani bayan dawowarsa daga karatunshi na Digiri na Biyu daga Maleysia, ya kama aiki da kamfanin sarrafa Leda na Plasmatix Nigeria Limited a inda ya rike mukamin Shugaba, watau General Manager.

Ya shahara matuka wajen koya darasin kimiya na Physics wanda ya zama gagara gasa tsakanin sauran malamai.
Abdulrashid Abba Ali mamba ne na Cyber Security Expert Association of Nigeria, Mamba ne a Teachers Registration Council of Nigeria da Kuma EC-Council Membership a America.
Ya halarci tarukan karo sani na Kasa watau National Conference kan Cyber Security Experts Association of Nigeria CSEAN, Abuja. Da na Kasa da Kasa watau International Conference a Malaysia Open Source Conference Berjawa Time Square Hotel, Malaysia.

Hon. Abdulrashid Abba Ali, ya rike mukamai da dama da suka hada da; Mataimakin Shugaban Kungiyar Goruba Initiative Katsina; Secretary Board of Directors/Establishment Committee, Turaki Sani Memorial School, Modoji, Ring Road Katsina; Chairman Class of 1990 Government College Oldboys Association Katsina; Director Annur International Limited; President Katsina State Student Union (BUK), Nigeria; Mamba, National Association of Physics Electoral Committee (BUK) da kuma Mamba, Bayero University Electoral Committee.

Abdulrashid Abba Ali Mutum ne Mai kokarin kamanta gaskiya da adalci a duk in da ya samu kanshi. Yana kuma da kishin ci gaban alumma.
Allah ya albarkace shi da Mata da ‘Ya’ya. Ya na kuma da sha’awar Karance-karance, tafiye-tafiye, wasan kwallon kafa, kwallon hannu (Fives) da kuma Squash.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here