Ɗan takar gwamna a Jihar Kano a Jam’iyar PDP a zaɓen 2019, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheka daga PDP zuwa NNPP a hukumance.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Yusuf, wanda a ka fi sani da Abba Gida-Gida, ya sanar da sauya sheƙar ne a yau Lahadi a mazaɓarsa ta Diso, Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

A jawabinsa, Yusuf ya ce PDP da APC duk kanwar ja ce, inda ya ce jam’iyar ta ci amanar al’ummar Kano da jagoran ta, tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso duk da irin ɗimbin ƙuri’ar da su ka kaɗa mata a zaɓen 2019.

A cewar sa, matakin sauya sheƙar ya zamto mai muhimmanci duba da irin kiraye-kirayen da miliyoyin al’umma su ke yi na ya sauya jam’iyyar NNPP, wacce ta ke da manufofi na gaskiya na tserar da ƴan ƙasa da ga mawuyacin halin da su ke ciki.

Daily Nigerian Hausa ta fahimci cewa sauya sheƙar ta Abba Gida-Gida ta zamto sharar hanya ga Kwankwaso, wanda a ke tsammanin shima a ranar 30 ga watan Maris zai fice daga PDP zuwa jam’iyar NNPP, inda da ga nan zai tsaya takarar shugaban ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here