Al’mizan

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Ekiti a ranar 18 ga Yuni, 2022 yayin da kuma za ta yi na gwamnan Jihar Osun a ranar 16 ga Yuli, 2022.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wurin taron da ya yi da kwamishinonin zaɓe na jihohi a ranar Laraba a hedikwatar INEC da ke Abuja.

Yakubu ya ce an wallafa ranakun da aka aje na fara yaƙin neman zaɓe da sauran cikakkun bayanai kan jadawalin ranakun zaɓen da sauran ayyuka dangane da zaɓuɓɓukan biyu a gidan yanar hukumar da shafukan ta na soshiyal midiya.

Ya ce, “A tsarin zaɓuɓɓukan waɗanda za a yi ba a cikin kakar zaɓe ba, za a yi zaɓuɓɓukan gwamnonin Ekiti da Osun ne a baɗi.

“A bisa bin ƙa’idar mu ta bayyana ranakun zaɓuɓɓuka kafin lokacin su don bada dama ga dukkan waɗanda abin ya shafa su fara shiri da kyau tun da wuri, wannan hukuma ta amince cewa za a yi zaɓen gwamnan Jihar Ekiti ne a ranar Asabar, 18 ga Yuni, 2022.

“Za a yi zaɓen gwamnan Jihar Osun bayan wata ɗaya da yin wancan, wato a ranar Asabar, 16 ga Yuli, 2022.

“Mu na roƙon jam’iyyun siyasa da masu son tsayawa takara da su tabbatar da cewa sun gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwani babu wata hatsaniya, sannan kuma bayan hakan su gudanar da kamfen ɗin zaɓe a cikin lumana.”

Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa a bisa tsarin jadawalin ranaku da ayyukan zaɓuɓɓukan biyu, INEC za ta fitar da sanarwa kan zaɓen gwamnan Jihar Ekiti a ranar 3 ga Janairu, 2022.

Haka kuma hukumar ta aje daga 4 ga Janairu zuwa 29 ga Janairu, 2022 a matsayin ranakun da za a gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwani na jam’iyyu a jihohin.

Ya ce za a fara yaƙin neman zaɓe na jam’iyyun siyasa a ranar 20 ga Maris, 2022 a gama a ranar 16 ga Yuni, 2022, yayin da kuma za a fitar da jerin sunayen ‘yan takara na ƙarshe a ranar 19 ga Mayu, 2022.

A game da zaɓen Jihar Osun kuma, za a fitar da jadawalin ranakun zaɓe kamar yadda aka tsara a ranar 15 ga Fabrairu, 2022.

Bugu da ƙari, zaɓuɓɓukan fidda gwani na jam’iyyu tare da warware rigingimun da ka iya tasowa za a gudanar da su ne daga ranar 16 ga Fabrairu, 2022 zuwa ranar 12 ga Maris, 2022.

Ana sa ran za a fara kamfen na zaɓe na jam’iyyu a jihar daga ranar 17 ga Afrilu, 2022 a gama a ranar 14 ga Yuli, 2022.

Yakubu ya ce an aje ranar 8 ga Afrilu, 2022 a matsayin ranar ƙarshe ta janye sunan ɗan takara daga zaɓe ko musanya shi da wani da jam’iyyu za su iya yi, sannan a ranar 16 ga Yuni, 2022 za a wallafa sunayen ‘yan takarar zaɓen gwamnan Osun.

Yakubu ya ce a shirin da ta ke yi domin nan gaba kaɗan, hukumar ta na nan ta na tsara yadda za ta gudanar da sauran zaɓuɓɓukan da ba na kakar zaɓe ba ne da kuma waɗanda na ƙarewar wa’adi ne kafin Babban Zaɓen shekarar 2023.

Ya ce yanzu haka har ma an soma aiwatar da ayyukan da aka tsara yi a jadawalin ranakun zaɓen gwamnan Jihar Anambra.

“Haka su ma na zaɓuɓɓukan Yankunan Ƙananan Hukumomin Babban Birnin Tarayya da za a yi a ranar 12 ga Fabrairu, 2022,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here