Advert
Home Sashen Hausa A SAKE DUBA DOKAR MAGANCE TSARO A KATSINA.....INJI KUNGIYOYIN FARAR HULA

A SAKE DUBA DOKAR MAGANCE TSARO A KATSINA…..INJI KUNGIYOYIN FARAR HULA

Hassan Male @Katsina City News

Gamayyar Kungiyoyin Farar hula reshen jahar Katsina sun yi Kira da a sake yin nazari dangane da dokar da gwamnatin jaha ta sanya don magance ayyukan ta’addanci a fadin jahar.

Jaridar nan ta yanar gizo Katsina Beat a ranar alhamis ta ruwaito cewar, shugaban Kungiyar Abdulrahman Abdullahi yace, dokar tafi shafar al’umma ne kawai maimakon Yan’ bindiga musamman ta bangaren hanyoyin sadarwa da kuma zurga zurga da iccen makamashi.

Sai dai yace, a makonni biyu na farkon dokar, an samu ragowar hare hare a fadin jahar.

“Ayyukan yan’ bindiga sun sake dawowa a hankali ne da Samun karin wadanda hare haren yan’ bindiga ke shafa fiye da lokuttan baya. Wannan manuniya ce cewar, yan’ bindiga sun samu sabbin dubarun kauracewa wadancan matakai.

” Da yawa mutane a yankunan karkara suna korafi kan dakatar da hanyoyin sadarwa a matsayin babban dalilin sake samun yawaitar karuwar ayyukan yan’ bindiga a yankunan karkara. Mun sani cewar, yan’bindiga kan iya shiga gari su share awanni ba tare da jami’an tsaro ko yan’ sa kai ba sun kai ma su agaji ba wanda hakan na faruwa ne dalilin datse hanyoyin sadarwa”, yace.

Dangane da hana shigo da itace, AbdurRahman yace, mutane na shan matukar wahala.

” Mutane a yanzu suna yanko itatuwa na kusa dasu wanda hakan ka iya haifar da matsaloli na hamada, saboda haka bayan matsalolin tattalin arziki da lamarin ya haifar, dole kuma a kalli matsalar muhalli domin da zaran mutane sun yanke itatuwan dake a muhallin su mafi kusa, to Allah ka dai ya san mai zai faru”.

Gamayyar ta Kungiyoyin Farar hular ta roki hukumomin tsaro da kuma gwamnati da su zo da wasu sabbin dubarun dakile ayyukan masu hada kai da yan’ bindiga da har yanzu su ke shigar masu da fetir cikin daji duk da tsatstsauran matakan da aka sanya.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...