A koma tsarin tsaro irin na da daga kowane matakin gwamnati – Buhari

Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya kamata a koma tsari “irin na da” domin samar da tsaro “a kowane mataki” na gwamnati a ƙasar mai fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Kazalika, shugaban ya koka cewa “duk sanda wani abu ya faru sai mutum ya garzaya fadar shugaban ƙasa”, yana mai cewa a da ba haka ake yi ba.

“Bayan na gama sakandare na shiga aikin soja, daga laftanar zuwa janar, na san a kowace ƙaramar hukuma akwai majalisar tsaro ƙarƙashin basaraken gargajiya da shugaban ‘yan sanda na yankin da baƙi makiyaya da ‘yan kasuwa,” in ji shi.

“Akwai irin wannan majalisar (ta tsaro) a duk faɗin Najeriya. Suna kai rahotonsu ne ga gwamnan jiha, sai dai idan akwai wani abu muhimmi sai a je wajen shugaban ƙasa.

“Ina ganin ku je ku gyara tsarin tsaro…saboda a yi maganin matsalar a kowane mataki. Yanzu mun shantake, duk sanda wani abu ya faru sai mutum ya bazama zuwa fadar shugaban ƙasa.

“Kamar yadda na faɗa, za mu dirar wa masu aikata laifuka. Wajibi ne a dawo wa da mutane ƙwarin gwiwa a kan gwamnati a cikin mako shida masu zuwa, idan ba haka ba kuma za mu shiga cikin yunwa saboda manoma ba za su iya komawa gonakinsu ba.”

Buhari ya yi waɗannan kalamai ne fadarsa da ke Abuja a makon da ya gabata, inda ya bayar da umarnin a harbi duk wanda aka gani da ɗauke da bindiga ƙirar AK-47.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here