Daga Wakilin Dimokradiyya na Jahar Katsina Usman Salisu Gurbin Mikiya

Shuwagabancin Jami’ar Umaru Musa Yar’adua dake Jahar Katsina, ya sake kama Manyan macizai masu yawa a cikin Makarantar.

Acikin wata sanarwa da aka rarrabawa Manema Labaru, tace an dauki matakin a matsayin wani kokari na magance macizai da sauran Dabbobi masu hadari a cikin Jami’ar.

Sanarwar tace an samu nasarar ne, a lokacin wani feshi data gudanar a dukkanin lungu da sako na Jami’ar.

Baya ga feshin da Jami’ar ke gudanarwa, ana Kuma share dukkanin daji da dasa itatuwa domin kyawon Jami’ar, gami da korar macizai da mugayen Dabbobi domin kiyaye Lafiyar Mazauna cikin ta.

Sanarwar ta kuma bukaci Dalibai da Sauran dukkanin Mazauna Jami’ar, dasu kawo duk wani motsin mugayen Dabbobi da basu gane mawa ba, domin daukar matakin gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here