A KASA A TSARE: Gwamna Masari ya kai ziyara don ganin yanda Aikin Titin ƙasa ke gudana a Kofar Kaura…

Gwamnan Katsina Aminu Masari tare da Injiniyan da ke kula da Aikin a wajen

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya kai ziyarar bazata a Unguwar Kofar Kaura Katsina don duba yanda aikin Babban titin Zamani Underpass ke gudana,

Gwamnan tare da ‘yan rakiyarsa sun zagaya ko ina,inda aikin ya shafa, domin ganewa idonsu.

A ranar alhamis din 24 ga watan da ya gabata ne, Gwamnan ya Kaddamar da Manya-manyan Aiyukan Titunan da zasu lashi fiye da Naira Miliyan Dubu Dari Hudu da Hamsin, a waje biyu, Kofar Kaura da Kofar Kwaya, duk acikin Birnin Katsina, domin rage cunkoso, a kwaryar garin.

Kamfanin TRIACTA ne ya amshi kwangilar aikin inda yanzu haka, ake cikin yin na Bangaren kofar Kaura, kafin daga bisani a fara na Kofar kwaya…”aikin na gudana lami lafiya, kuma a kullum ba tare da wani jinkiri ba, mai yiyuwa hakan yanada alaƙa da Alkawari da kamfanin ya dauka na cewa zai kammala ayyukan a cikin shekara daya…”

Inji wani Mai sana’a a inda aikin yake gudana.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here