A karon farko an rantsar da Kwamared Hauwa Sulaiman wacce aka fi sani da Jidder a matsayin shugabar ɗalibai ta jami’ar gwamnatin tarayya da ke garin Dutsinma, FUDMA anan jihar Katsina.

An rantsar da Kwamared Jidder ɗin ne bayan da mai riƙon shugaban ƙungiyar ta ɗaliban jami’ar Kwamared Saleh Aliyu Damaga ya kammala jami’ar, inda aka rantsar da Kwamared Jidder wacce ita ce mataimakiyarsa.

Wannan dai shi ne karon farko da aka samu ɗaliba mace ta shugabancin kungiyar dalibai a tarihin jami’ar ta FUDMA.

Kwamared Hauwa Sulaiman
Haka kuma wannan lamarin ba kasafai yake faruwa ba musamman a jami’o’in Arewacin Najeriya.

Hakazalika a iya cewa ma wannan ne karo na uku da hakan ta kasance a yankin, tun bayan da Amina Yahaya ta zama shugabar dalibai a jami’ar Sokoto a shekarar 2016 da kuma fitacciyar ‘yar siyasar nan Naja’atu Bala Muhammad da ta ja ragamar shugabancin kungiyar dalibai ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sama da shekaru talatin da su ka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here